YADDA JAM IYYAR PDP TA RIKA NEMAN DAN TAKARAR SANATA

0

YADDA JAM IYYAR PDP TA RIKA NEMAN DAN TAKARAR SANATA

Daga wakilan Taskar labarai

Wani labari da ya zo ma Taskar labarai kuma ta tabbatar dashi shine yadda jam iyyar PDP ta Rika neman Wanda zai Mata takarar Sanata Katsina ta tsakiya Ido Rufe.

Binciken mu ya tabbatar Mana da cewa Alhaji ibrahim Dankaba..da ya sayi fom din da kudinsa ya cike

Maigidansa a siyasance​ Brista shema tsohon gwamnan Katsina ya fada masa cewa .za a karbi kujerar daga wajen sa..a ba’ wani. Da yake Yana biyayya gare shi ya kuma amsa Masa..ya yarda

Ance bayan kammala zaben fitar da gwamna a PDP Wanda Yakubu lado yayi nasara .sai aka fara neman wa za a ba takarar Sanata a Katsina ta tsakiya?

An tuntubi injiniya Muttaqa Rabe darma.. yace baya bukata.aka kuma tuntubi Ahmad Aminu..shima yace ya gode , daga Nan aka tuntubi Alhaji sada ilu shima yace a Kai kasuwa.

Dukkaninsu Taskar labarai ta tuntubi wasu na kusa dasu sun tabbatar da anyi Haka .akwai mutane hudu da jaridar da Bata tabbatar ba..Amma su ma aka ce an masu tayi suka ce ..akai kasuwa!!!

Wadanda mutanen da ake Jin an Yi ma magana sun Kai bakwai..duk suna kin amincewa

Kowannensu jaridar ta tabbatar da cewa sunki amincewa ne Don Basu son suyi aiki tare da yakubu lado.wanda PDP ta tsaida a matsayin Dan takarar gwamna.wanda suna ganin tafiya tare dashi zata zubar masu da kima da mutumci..zata kuma lalata masu tarihin siyasar su.

Da kowa yaki amsa ne ..aka amince a baiwa” Alhaji Hamisu Gambo Dan lawan Katsina…Wanda Ibrahim Lawal Dankaba ya janye Masa..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here