AN ZABI ZAINAB BAGUDU A MATSAYIN DARAKTA A KUNGIYAR MASU YAKI DA CUTAR DAJI TA DUNIYA

0
455

AN ZABI ZAINAB BAGUDU A MATSAYIN DARAKTA A KUNGIYAR MASU YAKI DA CUTAR DAJI TA DUNIYA

 

A yayin gudanar da babban taron duniya na Kungiyar yaki da cutar Sankara wato Daji (UICC), na bana da ya gudanar a birnin Kuala Lumpur na Kasar Malaysia ne aka zabi Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Zainab Shinkafi Bagudu a matsayin Babbar daraktar Kungiyar na wa’adin shekaru biyu tare da wasu mutane 12 a matsayin membobi na wannan Kungiyar, wadda ta shekara 85 ta na yaki da cutar Daji.

 

Rahoton musamman daga zauren taron, ya tabbatar cewa Dr Zainab ta sami wannan nasarar ne, tare da karfafawar maigidanta Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, da Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya Aisha Buhari, da kuma Karin goyon baya daga Ministocin Harkokin Wajen Nijeriya – Geoffrey Onyeama da Khadija Abba Ibrahim, da kuma Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole.

 

An dai bayyana cewa namijin kokarin Dr Bagudu, wacce likitar kananan yara ce, gami da yadda ta ta kafa babbar gidauniyar wayar da kai da kulawa da masu cutar kyauta a Nijeriya, mai suna ‘Medicaid Cancer Foundation (MCF), ya sa aka bayar da sunanta, har kuma ta yi zarra a tsakanin ‘yan takarar wannan mukamin.

 

Ana dai saran wannan zabin na Dakta Zainab zai taimaka wajen yaki da wannan cutar ka’in – da – na’in, kuma daga ayukkan da ta gabatar wannan Kungiyar ta na fatan samun raguwar wannan matsala da kashi 25 kafin nan da shekara ta 2025.

 

Hedikwatar kungiyar ta UICC, wadda ke birnin Geneva a kasar Switzerland, tana da yawan membobi fiye da 1000 a tsakanin kasashe 160, inda kuma take hyin hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar kula da makamashi ta duniya da kungiyar kula da tattalin arziki ta duniya da sauran manyan kungiyoyi na duniya masu wayar da kai dangane da cutar ta Daji.

 

Rahoton ya kara fitar da cewa a wannan shekarar kadai akalla mutane Milyan takwas za su iya mutuwa matukar ba su sami kulawar da ta kamata dangane da cutar ba, inda ake ganin yawan mace-macen zai haura Milyan 13.2 kafin shekarar 2030, sannan aka nuna cewa Nahiyar Afrika, wacce take baya a fagen wayar da kai gami da kulawa da masu cutar, za ta fi samun kanta cikin tsaka mai wuya.

 

A yayin da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da zaben Dakta Zainab Shinkafi Bagudu, Shugaban Gangamin Wayar da Kai dangane da cutar Daji a Nijeriya Farfesa, ya bayyana wannan zaben nata a matsayin wata dama ga kasashe masu tasowa su yaki cutar, don haka ya yi kira a gaggauta aiwatar da dokar yaki da cutar Daji ta kasa da aka kaddamar a cikin shekarar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here