MAKIRCIN SIYASA A ZABEN FITAR DA GWANI NA DAN MAJALISSAR JIHA A KARAMAR HUKUMA MANI

0

MAKIRCIN SIYASA A ZABEN FITAR DA GWANI NA DAN MAJALISSAR JIHA A KARAMAR HUKUMA MANI

 

Daga wakilan Taskar labarai.

 

Wani bincike da mukayi da gano yadda aka yi amfani da kullin makirci aka kayar da dan takara mai neman kujerar majalisar jiha a karamar hukumar Mani. Dan takarar da aka kayar wanda yayi takara da Aliyu Sabiu Muduru Sunansa Yunusa Muhammad yana da digiri har guda uku, malami ne jami’ar Umaru Musa Yar’adua.

 

Bayan sayen fom da cika shi da za a tura takardunsu Abuja sai aka zare na sakandare na shi, daga Abuja ofishin APC na kasa sai wani kwamiti yazo yace , Yunusa Muhammad daga karamar hukumar Mani ba zaiyi takara ba, Don baya da takardun kammala sakandare.

 

Gwamnan Katsina yace a a bata sabuwaa dai bincika aka kira Yunusa Muhammad yazo da duk takardun sa orijinal aka duba aka ga cewa ashe zare takardun aka yi a takardun da aka tura Abuja.

 

Sai kwamitin yace shike nanyana iya takara, amma ashe ‘yan kwamitin nasu gyara ba a takardun da za a baiwa malaman zaben da za su je kananan hukumomin.

Ranar zabe Asabar 6/10/2018 malaman zabe suka isa Mani suka fara da kiran sunayen wadanda zasu yi takara, ba sunan Yunusa Muhammad nan yace bata yiwuwa aka yi carko carko aka fara buga waya.

Wannan jinkiri da tsaiko da cece a ce, sai aka fara shaida wa deliget cewa ai gwamnati ce bata son Yunusa Muhammad yaci zabe ,shi yasa aka ce bai cancanta ba daga nan sai wasu deliget suka ce to ai tunda gwamnati bata sonsa muma bama yinsa. Sai kuma aka yadawa deliget cewa ya janye sai rudu ya shiga.

See also  Zaɓen gwamna na Kogi: Ban ce na zaɓi Dino Melaye a matsayin ɗan takara ba - Atiku

A can kuma kwamitin zaben suna buga waya neman umurnin ana iya zaben da Yunusa ko a a, dai-dai lokaci an ruda masu zabe.

Daga baya aka ce ayi zaben da Yunusa Muhammad duk da rudun da rashin tabbas sai da Yunusa Muhammad yazo na biyu da kuri’u sama da dari da ashirin Ali Sabiu Muduru yaci da kuri’u sama da dari da arba’in.

 

Wata majiya tace hatta kantoman Mani an masa barazanar cewa in ya kuskura Yunusa Muhammad yaci zabe to a bakin kujerarsa. Wannan yasa dole shi ma yayi abin da zai iya don ganin Yunusa ya fadi zaben.

 

Wani yace duk jita-jitar da aka rika yadawa na Yunusa ya janye gwamnati bata tare da Yunusa duk yaran kantoman Mani ne.

Wasu deliget sun tabbatar wa da TASKAR LABARAI cewa . kantoman ya kira su ta waya yace su zabi Ali Sabiu Muduru shi ne dan takarar sa.

 

Shi Yunusa Muhammad ya dade yana siyasa tun APP kuma bai taba yin jam’iyya mai mulki ba. Na kusa da minista Hadi Sirika ne, wanda ake Jin wannan kulli da aka yi masa rikicin cikin gida ne kusancinsa da Hadi Sirika yaja masa, ana ganin shi ne ke daukar nauyin sa, kuma biyayyarsa a gare shi take.

 

Lokacin bada kantomomi ma, majalisar jiha taki amincewa da wanda Hadi Sirika ya roka a baiwa kantoma daga karamar hukumar Dutsi, ‘yan majalisar suka ki wanke shi, sai dai canza shi aka yi da wanda aka ce biyayyarsa na ga gwamnatin jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here