-
Wani Gwamnan APC A Arewa Ya Karbi Toshiyar Bakin Dalar Amuruka Miliya Biyar (5 million Dollars) A Wasu Kwangiloli Da Ya Bayar
Fassara Abdurrahaman Aliyu
Kemara sirri ta nuna wani gwamna daga cikin gwamnonin arewa maso yamma yana karbar toshiyar baki kan wasu kwangiloli da ya bada a gwamnatinsa.
Wannan gwamna Wanda yanzu haka yake neman takara karo na biyu a karkashin jam’iyyar APC yana tsaka mai wuya, wanda hakan kan iya sawa ya rasa tikitinsa.
A bidiyo kala uku da wakilin jaridar Daily Nigeria ya gani, ya nuna cewa gwamnan ya amshi kudaden a ranaku mabambanta wanda yawan kudaden ya kai kimanini dala Amuruka Miliyan Bihar (5 Million Dollars).
A daya daga cikin bidiyon an nuna gwamnan ba hula a Kansa yana ganawa da dan kwangilar, bayan sun gama ganawa ya mashi bamdiran daloli ya sanyasu a aljihun rigarsa da kuma wandonsa, ya yi gaba.
A bidiyo na biyu kuma da Wakilin Jaridar ya kalla an nuna gwamnan da babbar riga da hula inda ya amshi toshoyar bakin dalar Amuruka miliyan uku, wanda ya kama kashi ashirin da biyar na alawajar kwangilar da ya bayar.
Jaridar Daily Nigeria ta yi kwakkwararn bincike kan bidiyon domin ta tabbatar da sahihancinsa ko akasin haka, amma daga karshe ta gano cewa bidiyon na gaskiya ne kuma yana da sahihanci.
Daya daga cikin tawagar kwararru na duniya kan yaki da con hanci da rashawa ya tabbatar da cewa wannan bidiyo ba na bone ba ne, abin da ke cikinsa gaskiya ne.
Bayan sauraren hirarrakin da ke cikin bidiyon an tabbatar cewa, maganganun da aka yi sun yi daidai da abinda hoton bidiyon ya gwada.
Bayan samun bayanan tabbatarwa daga kwararru Jaridar Daily Nigeria zata mika bidiyon ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin daukar matakin da ya dace.
Yaki da con hanci da rashawa da kuma ta’addanci shi ne abin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta sa gaba, wanda shugaban ya sha fadin haka a taruka da dama da yake halarta.
Haka kuma an ga iron wannan kudirin a zahiri, musamman yadda aka cire Sakataren gwamnatin Tarayya Babachir Lawal da kuma tsohon shugaban hukumar NIA Ayodele Oke, duk da cewa ‘yan Jam’iyyar adawa suna ganin cewa an fi matsa masu fiye da wadada ke cikin gwamnati.
Jaridar Daily Nijeriya zata yi tsayin daka wajen ganin cewa Shugaba Muhammad Buhari ya dauki mataki kan wannan gwamna na dakatar da shi daga yin takara karo na biyu, musamman ma saboda tabbatar da kudirinsa na kakkabe cin hanci da rashawa a kasar nan.
Wata majiya ta tabbatar da cewa shugaban kasa zai sa a cireshi ko kuma a maye gurbinsa da wani a matsayin Dan takara jam’ iyyar APC a jihar sa, ko kuma ya sauka da kashin kansa.
A wata majiyar kuma da samu Jaridar Daily Nigeria ta tabbatar da cewa gwamnan ya zauna da wasu na kusa da shi domin su shirya yadda za su karyata bidiyon kafin abin ya karade Al’umma.
Koma dai ya ke nan Jaridar Daily Nigeria zata cigaba da kawo maku bayanai kan wannan balahatsa.