Sanata Yakubu Lado Danmarke: Tsakanin Gaskiya Da Karya (1)

0

Sanata Yakubu Lado Danmarke: Tsakanin Gaskiya Da Karya (1)

 

Daga Abdurrahman Aliyu

 

Sanata Yakubu Lado Danmarke shi ne wanda jam’iyyar PDP ta tsayar a matsayin wanda zai mata takarar gwamna a zaben 2019.

 

Kafin kaiwa ga wannan matsayin sanata Yakubu Lado ya rike mukamai da dama na siyasa wadanda suka hada da Kamsila da ciyaman har zuwa Sanata mai wakiltar kudancin Katsina.

 

A lokacin da ya yi sanata a Jam’iyyar PDP daga 2007 zuwa 2011, ya zama mamba a kwamitoci da suka hada da na albarkatun ruwa da na zirga-zirga da kuma na wasanni.

A lokacin da ya ke shugabantar kwamitin zirga-zirga ya kalubalanci Ma’aikatar zurga-zirgar da rashin yi mashi bayanin yadda ta sarrafa kudaden da ta ba kamafanin CCECC kwangilar sabunta hanyoyin jiragen kasa zuwa na zamani, wanda kudin kwangilar ya kama dala biliyan takwas da digo uku.

Haka kuma a lokacin yake Shugabantar kwamitin ne ya kawo batun bayar da dama ga Yan kasuwa domin su saka hannayensu wajen huddar jiragen kasa a Nijeriya, a watan Nuwambar 2009.

 

Irin wadannan abubuwa da ya gudanar na cigaban al’umma sun taimaka mashi sosai wajen samun farin jinin shiga takarar gwamna a 2011 bayan ya bar jam’iyyar PDP ya shiga sabuwar jam’iyyar CPC. A lokacin sun yi takun saka da gwamnan jihar Katsina na yanzu wato Alhaji Aminu Bello Masari inda kowanen su yake ikirarin shi jam’iyya ta tsada a lokacin.

 

Wannan bincike zai dubi wasu abubuwa ne guda biyu dangane da cancanta ko rashin cancantar Sanata Lado a matsayin dan takarar gwamana, kuma alkalancin ya na ga masu zabe, kamar yadda wannan jaridar ta Taskar Labarai ta alkawarta maku wajen yin nazarin ‘yan takarar da jam’iyyu suka tsayar.

 

HATSARIN SANATA LADO A SIYASAR KATSINA

 

Duk wanda aka ce ya fara siyasa tun daga Kamsilia har zuwa Sanata to ko shakka babu ya wuce a kirashi da karamin dan siyasa ko kuma dan dagajin siyasa, ko kuma wani wanda bai da barazana, Yakubu Lado zai iya zama barazana sosai ga gwanatin APC musamman kasancewarsa matashi kuma wanda ake ganin ya rungumo kudi da zai iya amafani dasu wajen bata ruwa ko ba dan ya sha ba.

See also  MAGANIN RAGE DA HANA ZUNUBI

 

Haka kuma zai iya jazawa gwamnatin asara kashe kudade da yawa musamman wajen yakin nema, tun ma ba a yankin sa ba da ake ganin gwamnatin ta yi karfa-karfa wajen tsayar da Dan takarar Sanata wanda ake ganin ba shi jama’a ke so ba, wannan zai taimaka mashi sosai wajen samun nasara a wasu kananan hukumomin yankin goma sha daya.

 

Wata dama da Lado zai iya samu ita ce hada karfi da karfe da wasu daga cikin wadanda suka fadi zaben fita da gwani da suka yi tare, da kuma hasashen da ake da shi na cewa, a shiyyar Katsina ta tsakiya ma Sanatan da aka tsaida ana ganin wanda jam’iyyar PDP ta tsayar ya fi nagarta, wannan ma wata dama ce da tana iya taimaka mashi ya kai ga nasara.

 

Sai kuma kudurorin da ake gani ya kawo a lokacin da yake Sanata, wanda suna da muhimmanci sosai, musamman ta bangaten raya kasa da taimakon matasa.

 

Wata dama kuma da zata iya taimaka ma shi ita ce fitar da wanda zai mashi mataimaki daga cikin mutane masu nagarta wadanda ake kyautatawa zato a jam’iyyar PDP, wanda hakan zai kara kawo masu farin jini ga jama’a.

 

Za mu kwanan nan sai rubutu na gaba in da zamu diba Nakasu da kuma Illolin Tsayar Da Sanata Yakubu Lado a matsayin dan takarar gwamna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here