Mai doki ya koma kuturi Yadda MAJIGIRI A MATAIMAKIN LADO? !!

0

MAJIGIRI A MATAIMAKIN LADO?

Yadda Mai doki ya koma kuturi!!

Daga wakilan Taskar labarai

Ta tabbata yakubu lado ya dauki Salisu majigiri a matsayin Wanda zai Masa mataimaki ..wani bincike da Taskar labarai tayi ta gano cewa amsar wannan matsayin kamar wani ci baya ne ga majigiri…Wanda yake shugaban jam iyyar PDP na jaha.

Wata majiya ta tabbatar Mana cewa daga cikin PDP akwai wadanda suka so shi majigiri yayi takarar gwamna a karkashin jam iyyar …har wani yayi alkawalin cewa idan shine zai Yi takarar zai amfani da alakarsa da wasu gwamnoni ya Tara gudummuwar da ta Kai ta Rabin bilyan a fara yakin neman zabe da ita..

Amma uban jam iyyar PDP ibrahim shema ya kafe cewa lallai a kyale ma yakubu lado takarar..

Kafin a fito da majigiri wata majiya ta tabbatar wa Taskar​ labarai cewa sai da aka tuntubi wasu mutanen suka ce a Kai kasuwa ..

Jaridar Katsina Post ta kawo labarin wasu ada aka fara tsammanin cikin su za a baiwa Daya…daga cikinsu.

Takarar yakubu lado a PDP ta jawo CeCe ku ce da yawan gaske ..Wanda har ta kai wasu jiga jigai a jam iyyar ta PDP suka fice daga cikin ta..suka koma APC

Wasu kuma suka ce zasu tsaya a ciki su yi ma PDP abin da tayi masu.. zasu Mai da Buki.

Binciken Taskar labarai ya gano a siyasance Katsina ba ta taba Mai bikin jinin takara ba..kamar yakubu lado ana jifarsa da maganganu kala kala

Ana ganin hadin takarar sa da majigiri kamar ..kamar gauraya man gyada ne ..da Ruwan sanyi..

Lokaci ne .zai haska ka ya tafiyar zata Kama..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here