RIKICIN GIDAN REDIYON VOA

0

RIKICIN GIDAN REDIYON VOA

Yadda aka kashe naira miliyan hamsin don binciken miliyan uku!

Daga Taskar Labarai

Wani bincike na musamman da Jaridar Taskar Lanbarai ta yi a kan rikicin da ya kai ga korar wasu ma’aikatan gidan rediyon VOA Hausa saboda amsar wasu kudi daga hannun wani gwamna a Nijeriya.

Wanda jaridar Daily Trust ta ce gwamnan Katsina ne Alhaji Aminu Bello Masari, amma kakakin Masari Abdu Labaran ya karyata, yace wannan​ zargin da ake ma gwamnansa ba gaskiya bane.

Taskar Labarai ta gano kudin da aka bayar yawansu ya kai miliyan uku. Wanda gwamnan ya bayar kyauta ba da wata manufa ba, amma da yake amsar kudin ya saba ka’idar hukumar gidan rediyon.

VOA ta kafa kwamitin bincike , binciken da ya lakume sama da naira milyan hamsin don kokarin gano gaskiyar me ya faru, dama wasu bayanan da allura ta tono garma.

Misali wanda ya tunkudo binciken Mr Ken shima sai da ta ci shi, inda bayanai suka nuna yana wasu almundahana da coge don ya samu kudi kuma binciken ya fada har a kansa, aka same shi da laifi, yana cikin wadanda aka sallama.

See also  Dauda Kahutu Rarara zai gurfana a Kotu

Lamarin sai ya zama fassarar in zaka gina ramin mugunta gina shi gajere. Mr Ken ya gina shi da zurfi suka fada a tare.
Taskar Labarai ta tabbatar an gayyaci hukumar binciken cikin gidan Amurka na FBI suka yi binciken, wanda kuma suka zo Nijeriya Don binciken.

Wata majiya tace har gwamnan​ da ake zargi an yi magana dashi, ya bada nasa bahasin. Binciken Taskar Labarai ya tabbatar an kashe kudade sama da miliyan hamsin don gano gaskiyar abin da ya faru na amsar kudi naira miliyan uku a kudin Najeriya.

Majiyarmu tace yanzu binciken ya shiga babi na biyu wanda shi ne ko an bayar da kudin ne da niyyar toshiyar baki? Idan ta tabbata da haka, to gwamnatin Amurka na iya daukar matakin wanda ya bada kudin kar ya kara shigar mata kasa ko ya nemi izni za a hana shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here