ZA AYI FASA KWAURIN MAGUNGUNA DA AKA HADA DA NAMAN. MUTUM..
Daga Abdurrahaman Aliyu
Hukumar hana fasa kwari ta kasar Koriya ta bayyana cewa ta a ranar 30 ga watan Satumbar 2019 ta kama gurbatattun magungunan da ake shigowa da su daga kasar Chana sama da dubu biyu da dari bakwai da hamsin da daya (2,751) wadanda aka hada su ba bisa ka’ida ba, magunan sun haxa da maganin tayar da kwanji na jiki da maganin ciwoin suga da maganin kansa, da sauran magunguna makamantansu, wadanda aka shigo da su ta barauniyar hanya.
Ma’aikatar Magunguna da abinci da Koriya ta Kudu sun bayyana cewa cututtuka sama da biliyan daya da dari bakwai da ke damun al’umma wadanda suka hada da ciwon anta duk ana bayar da mgungunan su ne a ysarin kwaya, wanda haka ya haddasa aikata manyan laifukan safarar kwayoyi da kuma kawo wa lafiya cikas.
Wanda yanzu haka hukumar na kan aikin tamtamce wa, wannan ya sa ake kira ga ma’aikatar lafiya ta kasa da huku!ar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da hukumarkula da lafiyar abinci da ta kula da ingancin kayayyaki, da su ta rika sa lura da kuma tantance duk wani magani da zai fito daga kasar Chana ta kowace irin hanaya musamman ma waxanda ake sanyo wa ta akwatin aiko sako na kasa da kasa. Da kuma sa ido kan yadda magungunan ke yaduwa a cikin kasa.