Dan majalissar Tarayya na jam’iyyar APC a Zamfara ya koma PDP.

0

Dan majalissar Tarayya na jam’iyyar APC a Zamfara ya koma PDP.

 

Lawal Hassan Dan’iya Dan majalissa mai wakiltar Kananan hukumomin Anka da Marafa ya ficce daga jam’iyyar APC zuwa PDP, ya bayyana cewa dalilinsa na ficewar da ceea jam’iyyar APC a Zamfara ta mutu kuma ba zata kara shugabancin jihar ba, ya nuna cewa ba abin da ke cikin jam’iyyar sai son kai da munaficci da kuma rashin girmamma juna, sannan shugabanin bada ganin darajar kowa.

 

Ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne bayan ya saurari ra’ayi mutanensa, in da daga karshe ya yanke hukuncin komawa PDP domin su hada karfi da karfe su ceto jihar Zamfara daga kangin rashin tsaro da rashin ayyukan yi ga matasa da suka yi wa jihar kakagida..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here