DAN GWAMNAN KATSINA YAYI AURE CIKIN DATTAKU

0

DAN GWAMNAN KATSINA YAYI AURE CIKIN DATTAKU

 

Daga Taskar labarai

 

A satin da ya gabata daya daga cikin ‘ya’yan gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari mai suna Ibrahim ya auri diyar gwamnan jihar Neja.

 

Auren an yi shi cikin mutumci da dattaku, mutane kadan suka je daga jihar Katsina kuma duk dangin Angon ne na kusa da kuma wasu Jami’an gwamnatin Katsina guda uku kacal.

 

Lokacin daurin auren gwamnan baya kasar yana wata tafiya ta aiki a kasashen waje, don haka bai halarta ba, bai kuma tura wani babba a cikin gwamnatin ya wakilce shi ba.

 

Wannan shi ne karo na biyu da gwamnan ya bada aure yana rike da matsayinsa na gwamnan Katsina amma ba wani shagali ko kakabi da yayatawa da za a san gwamnan yana buki.

 

Ya aurar da diya yana gwamna dansa kuma yayi aure, amma duk a cikin dattaku aka yi hidimar. Wannan ya saba Al’adar da aka saba gani ga gwamnoni wanda in sun tashi hidimar ‘ya’yansu kafa ta samu ta facaka da dukiya, da sanya wa talakawa wadanda ke son auran da ‘ya’yansu amma basu da hali damuwa.

See also  Karrama Wasu Muhimman Mutane a Jahar Katsina

 

Aminu Masari ya tsara wani tsari mai tsauri wanda ya hana ‘ya:yansa na ciki da na jini kuskurar amfani da matsayin da yake sama don samun abin duniya.

 

Wannan ya sha bamban da wasu masu rike da mukaman da akan baiwa ‘ya yansu da na kusa da su kyaututtuka na fitar hankali, ko kwanan nan wani babban a gwamnatin Katsina wani zababbe (Mai mukamin da aka zabe shi) ya sai ma dansa mota ta miliyoyin naira ya ba shi kyauta don yaron yaji dadin rayuwarsa ya wataya ya more kuma har ya fara fantamawa da abinshi cikin gari.

 

Irin wadannan duk baka samun su ga ‘ya’yan Masari ko ‘yan uwansa na jini wanda abin a jinjina masa ne a wannan barayin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here