YAUSHE ZA AYI ADALCI A HUKUMAR SUFURI TA JIHAR KATSINA (KTSTA)?

0

YAUSHE ZA AYI ADALCI A HUKUMAR SUFURI TA JIHAR KATSINA (KTSTA)?

 

DAGA TASKAR LABARAI

 

Jama’a sun zura Ido da kasa kunne suga yadda gwamnan Katsina zai yi adalci a hukumar sufuri ta KTSTA dake Katsina.

An Dade ana surutun cewa hukumar ta mutu, wanda gwamnan ya sa ofishin odita janar na jiha ya binciki halin da hukumar ke a ciki.

 

Wasu mutane kuma sun kai korafin hukumar na bannata kudin gwamnati ICPC , wanda suma suka yi binciken hukumar ta KTSTA.

 

Binciken da ofishin odita janar na jiha yayi, ya mikawa gwamnati shi inda rahoton ya samu wasu Jami’ai na hukumar da laifi dumu dumu.

Gwamnatin Katsina ta dauki matakin ladabtar da duk ma’aikacin da aka samu da laifi Inda aka canza masu wajen aiki daga hukumar ta KTSTA zuwa wasu ma’aikatun don a ladabtar dasu .

Amma abin mamaki shugaban hukumar wanda yake dan siyasa ne Alhaji Babangida Nasamu wanda shima rahoton ya same shi da laifi, shi ne kadai wanda ba abin da aka yi masa, amma duk wanda laifin ya shafa an ladabtar dashi ban da mutum daya shi ne Babangida Nasamu.

 

Wannan mataki na kin ladabtar da Babangida Nasamu na daga abin da ake ta tattaunawa akai hatta a ofishin odita janar na jiha da suka yi binciken. Kuma jama’a na yi wa gwamnatin wata mummunar fassara akan cewa, Gwamnatin bata ladabtar da ‘yan siyasa wadanda ta nada ko da kuwa wane irin laifi ake zarginsu da aikatawa.

 

Iyalai da ‘yan uwa da abokan arzikin wadanda waccan ladabtar wa ta shafa suna ta maganganun kuma sun sa ido suji me zai biyo baya? Ga wanda suke zargin shi ne kanwa uwar gamin laifin da ake zargin su akai har akai masu ladabtarwa.

 

Lamarin na kara jama wani attajirin Katsina Cece ku ce inda ake cewa shi ne ya daure masa gindi saboda shi ya sa baya tabuwa duk da an ladabtar da duk wadanda rahoton ya zarga da yin ba dai dai ba.

 

Editocin Taskar labarai sun ga wani bangaren rahoton wanda bayanan da ke a cikinsa babu dadin ji. Wani Jami’i a hukumar ICPC ya tabbatar wa da TASKAR LABARAI cewa sun yi bincike akan hukimar kuma sun tattara muhimman bayanai.

 

Taskar labarai ta rubutawa ICPC a hukumance cewa, suna bukatar kwafi na rahoton su.

 

jaridar har yanzu tana jiran amsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here