ABIN DA YA FARU A SHARA AR APC A JIYA.

0

ABIN DA YA FARU A SHARA AR APC A JIYA.

Daga Taskar labarai

Jiya anyi zaman kotu Wanda Yan takarar da suka sayi fom na APC karkashin Akida.suka shigar suna neman kotu ta haramta zaben ..saboda deliget da suka you zaben ba halastattu bane..

Kotun ta zauna Inda lauyoyin masu Kara duk sun halarta lauyan INEC ma ya halarta..Amma Babu lauya ko Daya daga APC ko jahar Katsina.

Alkaliyar tace ..tace kafin ta yanke matsayar bukatar da masu Kara suka shigar tana son ta San cewa wannan shara ar ..Bata Yi dai dai da wata da suka shigar a Babbar kotun tarayya dake Katsina ba?

Lauyan masu Kara yace Bata yi dai dai ba…!yace wadda suka shigar a Katsina .sun shigar da ita ne suna kalubalantar .zaben deliget deliget da akayi Inda suka ce ba ayi dai dai ba .ba a kuma bi kaida ba .Inda suke son kotun Katsina tace deliget din haramtattu ne.

See also  "DAGA APC NATIONAL HEADQUARTER ABUJA WAJEN RANTSAR DA SHUGABAN JAMA'IYYAR APC NA JIHAR KATSINA MAL. SHITU S SHITU"

Sai alkaliyar tace tana son a kawo Mata wannan bayanin a rubuce da rantsuwa. ta kotu. A dawo ranar 3/11/2018 ranar da zata bayyana matsayar ta Akan bukatar da suke nema.

Masu karar na neman, a soke ko jingine zaben fito da duk yan takarkaru da APC tayi daga Katsina…har sai an Gama sauraren kararsu.

Domin a cewarsu deliget din haramtattu ne ..duk abin da sukayi ya haramta..ko kuma kotu ta baiwa Dan Takarar su .. Abubakar samaila Isa Funtua..kamar yadda wani sashi na dokar zabe da suka dogara dashi ya ce.

Ana tashi kotu..jiga jigan APC akida suka Shiga wani taro a wani otal har cikin dare Basu kammala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here