ANA GARKUWA DA MUTANE A DAJIN RUGU

0
1216

ANA GARKUWA DA MUTANE A DAJIN RUGU

 

Daga Taskar labarai

 

 

Wani bincike da jaridar Taskar labarai ta yi sun gano ana tsare da mutane ma su yawan gaske a dajin Rugu wanda ya ha jihohin Katsina Kaduna da Zamfara.

 

Bincike ya tabbatar ma na da cewa a tsakanin kananan hukumomin Batsari da Safana akwai mutanen yankin da aka sace ake tsare da su cikinsu hadda wadansu kansiloli guda biyu.

 

Taskar labarai tayi magana da iyalin wata mata da aka sace daga Batsari ana neman a bayar da naira miliyan daya kafin a sako ta, ta fada wa iyalanta da cewa a dajin da ake tsare da ita sun kai su arba’in zuwa hamsin wadanda aka dauko daga wurare daban-daban cikin Katsina da wajenta aka kawo su sansanin ana amasar kudi kafin a sake su.

 

Taskar labarai ta gano cikin wadanda aka sace kwanan nan har da wani dan uwa na kusa ga Hajiya Husna mataimakiyar gwamnan Katsina ta musamman, amma shi an sako shi, Taska labarai basu tabbatar ba an bada kudin fansa ko a’a kafin a sako shi.

 

Amma dai an sako shi har ma an kawo shi gidan gwamnatin Katsina yayi godiya kamar yadda wadanda suka ganshi suka tabbatarwa da Taskar labarai.

A dajin Rugu na yankin karamar hukumar Dandume satar mutane ta zama ruwan dare kusan yana da wahalar gaske a dau kwanaki ba sace wani ko halaka wani ba.

 

Wannan ya sa ko kwanakin baya sai da wani Dattijo a yankin ya yi kira da manema labarai sukai dauki. Malam Adamu Ladan shugaban gidan rediyon Freedom Fm dake Kaduna yace, yankin Dandume ya zama abin tausayi.

 

Taskar labarai ta tuntubi kakakin yan sanda na jihar Katsina a kan sace-sacen yankin Batsari da Safana, inda yace a iya saninsu mutum biyu ne kansiloli ke hannun masu garkuwan, ko su ana gab da sako su, saboda an yi nisa da magana ta fahimta da masu garkuwan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here