LABO LEGAS (1912-1985)

0

LABO LEGAS (1912-1985)

 

Cikakken sunanshi Alhaji Abbas mutumen Galadunchi ne dake cikin garin Katsina.

Babban Dan Kasuwa, Manoni da kiwo.

A hirar da nayi da Muhammadu Nataala, Dan Alhaji Mamuda (Mudi) na Alhaji Labo Lagas Kangiwa Katsina, ya sheda mani cewa Marigayi Alhaji Labo Legas na daya daga cikin manyan yan kasuwa na farko a Katsina.

Kasuwancinshi ya hada da sayar da Turare, irinsu Mai Aku, Alkalin Goma, Dan Goma, Kafin-Kafi, Wardi, Kafi Sallama, Zawwati da sauran kayan masarufi.

Sarakuna da Hakimmai a wanchan lokacin babu shagon da suke sayayya irin wurinshi musamman lokacin bukukwan sallah.

Yana daya daga cikin mutanen da suka habbaka kasuwancin da ya sa bakin kasuwa da ita kanta kasuwar ta yi suna wanda yake binta har yau.

A lokacin idan yaje Arewa Textile Kaduna dauko kaya, idan babu ko sun yi karanchi sai ya wuce Lagos a chan yana iya yin wata Ukku kafin ya dauko kaya ya dawo gida.

Daga cikin abokai na kasuwancinshi sun hada da Alhaji Rabe Baika, Ahmad Mai Turare Kano mahaifi ga Zannan Kano Alhaji Aminu Ahmed Mai Turare Kano tare suke yawo a Kasuwar Kurmi suna sayar da Turare tun a wanchan lokacin.

See also  HOTO: Ziyarar da Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya kaiwa tsohon gwamnan Katsina Alhaji Sai’du Barda a gidansa, Alhaji Saidu Barda yana dan fama da jiki kwana biyu.

Saura sun hada da Alhaji Tukur Unguwar Jaji, Alhaji Magaji Unguwar Jaji, Alhaji Iyal Unguwar Shariffai Rafindadai.

Ya je aikin Hajj a kasa tun jirgin Makka bai fara zuwa Kano ba tare da Alhaji Abarshe (Mahaifin Barau Yaro) da Alhaji Halilu Kangiwa. Bai dawo ba sai a 1956 lokacin da jirgin Makka ya fara zuwa Kano.

Manomi ne sosai inda take da manyan gonakai guda Biyar a tsakanin Kukar Gesa, Kwarin Tama, Yandadi da Tsallatori.

Yana da manyan Shaguna guda biyar a tsakanin Kangiwa zuwa bakin kasuwa.

Yana da gidaje kimanin 90 a tsakanin bakin kasuwa zuwa Galadunchi. Akwai unguwa guda a nan Galadunci da ke dauke da sunanshi.

Mutanen da ke mashi hidima a wanchan lokacin ta gine gine, aikin gonarshi sai da ya mallaka masu gidaje kyauta saboda kyautatawa.

Rabin Makabartar Dan Takun Tsohuwa gonarshi ce inda ya bada ta a matsayin sadakatul jariya. Ya gina masallatai da rijiyoyi don neman lada daga Allah.

Ya rasu ya bar matan aure Ukku da yan uwanshi gida Ukku.

 

Kabir Umar Saulawa (PRO)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here