MUNGA CHANJI BUHARI/MASARI DODAR 2019.

0

MUNGA CHANJI BUHARI/MASARI DODAR 2019.

================================

Kai tsaye daga Muhammadu Dikko Stadium wajen taron Gangamin nuna godiya da goyon baya ga Buhari da Masari.

 

Kungiyoyin matasa da kungiyoyin mawaka da kungiyoyin masu shirya Fina, finan Hausa suka shirya wannan taron gamgami. Engr. Muntari Sagir Malumfashi ya dauki nauyin shirya wannan Gangami.

 

Kowa yasan irin gudumuwar da kungiyoyin matasan da kungiyoyin mawakan da masu shirya Fina, finan Hausa suka bada wajen fadakar da Al’umma aka kawar da gwamnatin PDP a zaben 2015.

 

Zaben 2019 ma sun sake dunkulewa wuri guda Don ganin jam’iyyar PDP bata dawo bisa mulki ba. In Allah ya yadda. Zasu cigaba da fafutuka don fadakar da Al’ummar kasar nan kada su yadda a yaudare su hannun Agogo ya koma baya.

 

Shugaban kasa M. Buhari yana iya bakin kokarin shi wajen ganin kasar nan ta hau turba mai kyau. Amma makiya kasar nan da Al’ummar ta suna ta kokarin ganin sun lalata wannan yunkuri nashi.

See also  Buhari ya ƙaddamar da fara aikin haƙo ɗanyen mai a Kolmani, yankin Bauchi da Gombe

 

Amma insha Allahu ba zasu samu nasara ba. Da ikon Allah kasa suke sai sun kunyata, Buhari/Masari sai sun maimaita da yaddar Allah. Wani abu daya dauki hankali shine dawowar Ali Nuhu tafiyar Apc ta Baba Buhari.

 

Kwana nan bayan zabukan fidda gwani aka ga Ali Nuhu tareda Dan takarar shugaban kasa kalkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019 tsohon mataimakin shugaban kasa H. E Alh. Atiku Abubakar.

 

Fara wancan tafiyar keda wuya ya gane yayi kuskure da yabi tafiyar da za’a cutar da Al’ummar Nigeria, yayi sauri ya dawo bisa hanya. Dama dashi akayi tafiyar 2015 ya bada gudumuwar shi wajen kawar da gwamnatin PDP

 

Report. Surajo Yandaki

 

Katsina State Apc Social Media Crew.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here