DAKATATTUN MA’AIKATAN KANANA HUKUMOMIN JIHAR KATSINA SUN GUDANAR DA JERIN GWANO
Sama da ma’aikata 792 ne na kananan hukumomi jihar Katsina, Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Aminu Bello Masari ta rike ma albashin wata 33 tunda ga Maris 2016 zuwa Oktoban 2018.
Wasu daga cikin wakilan sun yi tattaki zuwa ma’aikatar kanana hukumomi da masarautu daga nan suka wuce gidan gwamnati domin yi koke da nuna rishin amincewar abin da aka yi masu da, tun da Sun yi zama da Kwamishinan kananan hukumomi Hon. Abdulkadir Zakka in da suke kara tambayar shi, shin wai su mi suka yi da aka rike masu albashi tsawon wannan lokacin babu abinda ya fito daga bakin Hon. Abdulkadir Zakka sai cewa ya yi alal hakika babu dalili domin lokachin gwamnati ta tsininci kanta cikin halin rishin kudi ne wanda babu yadda su ka iya dole sai sun tsaida su, to kusa ni yanzu dai muna da kudi in kuka ga ba a biya ku ba to gaskiya son zuciya ne.
Bayan barin su Ma’aikatar Kananan hukumomi da Masarautu, sun wuce zuwa gidan gwamnatin domin yin koke ga Maigirma Gwamana Aminu Bello Masari inda su ka je gurin aka fada masu Masari bayanan sun yi hira da yan jaridu in da suka nuna halin kuncin da Wahala da bara da wannan gwamnatin ta Apc ta saka su tsawon wannan watanni 33 amma abin haushi, sai ga shi sun ji wasun su sun gani gwamnati ta tara mawaka yan Fim an yi rawar banjo an yi rawar nanaye, anyi rawar koroso an kashe makudan kudade.
To su ina kudadan su su fa yan jihar Katsina ne babu wanda yazo daga jihar Imo ko Legos dan me za a rike masu kudade bayan ana ta karya ana ceewa Masari mai adalci ne to su me yasa inda gaske ne baizai yi masu
adalci ba
Tabbas ba za su taba mancewa da abin da Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari ya yi masu ba domin dalilin shi wasu mata sun za ma jawarawa, wasu diya sun zama marayu
sun kuma yi Allah wadai da wannan gwamnati ta Aminu Bello Masari.
Daga Mai-iyali.