MASARI YA KADDAMAR DA CIBIYAR BUDADDIYAR JAMI’AR NAJERIYA (NOUN), TA FARKO A AREWACIN NIJERIYA

0
547

MASARI YA KADDAMAR DA CIBIYAR BUDADDIYAR JAMI’AR NAJERIYA (NOUN), TA FARKO A AREWACIN NIJERIYA

 

Gwamnan Bihar Katsina Rt. Hon.Aminu Bello Masari a yau litinin ya kaddamar da Sabuwar Cibiyar karatu na Budaddiyar Jami’ar Najeriya wadda akafi a turanche ake kirada da National Open university of Nigeria (NOUN), irinta ta farko a Arewacin Nijeriya a Mahaifar gwamnan wato garin Masari dake karamar Hukumar Kafur ta Jihar Katsina.

 

Ofishin yada labarai na gwamnatin Katsina sun riwaito babban maiba gwamna shawara a bangaren karatu Mai zurfi, Malam Bashir Ruwan Godiya yana fadin cewa kokarin gwamna masari na maido da martabar ilimi a fadin jihar Katsina yana haifar da da mai Ido, yace irin wannan yunkurin yasa yanzu haka, gwamnatin na kokarin Fadada jamiarta ta jiha don yin sabbin tsagayoyin Noma da lafiya, yace an gina tare da makare makarantar da kayan aiki kamar su computer guda 100 wanda aka hadasu da yanar Gizo Gizo, injin din bada wutar lantarki Mai karfin 100kvA, na’urar aikawada wutar lantarki Mai karfin200KVA , sabuwar mota kirar Toyota Hilux sabida zurga zurga yau da kullun, wajen Angina babban dakin karatu ginin tafiyar da shugabancin makarantar gamida Babban dakunan Daukar Karatu.

 

Shugaban jami’ar farfesa Abdullah uba Adamu, a jawabinshi ya tabbatar da cewa wananna ne Karon farko a arewacin Nijeriya da aka ginama jami’ar wananan katafaren cibiya, kanan aka makareta da kayan koyo da koyarwa na zamani.

 

Abdullah, ya yabama kokarin gwamna masari a fannin ilimi, kanan, yayi kira ga daukacin Jama’ar jihar Katsina dama kasa bakidaya da Su samu shigowa wanann Jami’a, domin Jami’ ar tana koyar da kwasakwasan da dukkkan Jami’O’i ke gudanarwa kanan yace takardar Jami’ar daya take da irin ABU, BUK, UDUTH da sauransu.

 

@katgovmedia sun ruwaito gwamna masari yana bayanin irin mummunan Halinda suka samu bangaren ilimi a jihar Katsina, amma a halin yanzu anfara farfado da ilimin Wanda a halin yanzu makarantar firamare ta mata dake Malunfashi tazamo ta Biyu a fadin kasarnan kamar yadda Rahoton hukumar Ilimin Baidaya(UBE) ta kasa tace.

 

Kanan ya Tabbatar da cewa gwamnatinsu zatacigaba da ba Jami’ ar goyon baya da tallafi don tabbatar da makarantar ta zauna da kafafuwanta, kanan ya Umurci kwamishinan mai kula da kananan Hukumomi da ya tabbtar kananan hukumomi sha 11 dake Yankin dan majalisar datttawa wato Funtua zone Sun dauki Nauyin karatun a kalla mutun 10 daga kowace karamar Hukuma, kanan yace suma yan majalisa daga yankin suma yakamata su dauki nauyin karatun wasu daga cikin mutanenda suke wakilta.

 

Filin da aka gina wannan Jami’ar dai wajene mallakar gwamnan wanda ya sadaukar dashi kyauta don wannan abin cigaba.

 

Director General

Katsina Media & Publicity

Ibrahim M Abdullah

5th November 2018

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here