YAN BINDIGA SUN KAI HARI A KANKIA
Daga Taskar labarai
Wasu Yan bindiga Bisa babura sun Kai Hari a Garin gachi ta karamar hukumar Kankia a jahar Katsina Inda suka hallaka wani Dan kasuwa Mai suna Nasiru mainasara Inda suka harbe shi har lahira suka kuma Yi awon gaba da diyarsa Yar shekaru goma Sha biyar Mai suna Aisha
Ance Yan bindigar wadanda ake zargin masu satar mutane ne Don neman kudin fansa sunje gidan mamacin ne da tsakar dare.
Rundunar Yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin har tace sun tura jami ansu na gaggawa wadanda sukan Kai dauki ga irin wannan yanayi.