AN SACE MATA DA GOYO A CHEDIYA TA BATSARI

0

AN SACE MATA DA GOYO A CHEDIYA TA BATSARI.

Daga Taskar labarai

A Garin cediya ta karamar hukumar batsari.a jahar Katsina .masu garkuwa da mutane sunje cikin dare a karshen makon ya gabata ..Inda suka Kai farmaki a gidan wani attajirin Manomi‚Äč a Garin Mai suna Alhaji Haro Wanda suka iske baya a gida sai suka tafi da matarsa Mai suna Aisha da diyarsu Mai Shan nono Mai suna maimuna .

Da zasu tafi sai suka rubuta lambarsu da gawayi a jikin bangon gidan suka ce a Kira su da ita har zuwa rubuta labarin nan ba a sako ta ba..kuma Babu wata takamaimar magana daga wadanda suka sace matar da diyar ta

See also  Ni Injiniya muhammad Nura Khalil, Ina mika sakon gaisuwata da Kuma godiya ga al'ummar jihar katsina

Haka Nan kuma Taskar labarai ta jiyo wasu mutane da kaki irin na soja sun tare motar wani dillalin shanu Mai suna iliya a tsakanin sabuwar hanyar ummadau zuwa tsaskiya Inda Inda suka tafi dashi. Cikin daji.

Dukkanin wadannan Rahotannin guda biyu rundunar Yan sanda basu ce komai ba akansu

Wakilan Taskar labarai na musamman a yankin suna gudanar da zurfin bincike Akan wasu laifuffukan irin wannan da ake zargin sun faru ko suna faruwa..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here