RAYUWA A INDA AKE TSARE DA WADANDA AKAI GARKUWA DA SU
“….NAGA YAN TAGWAYEN ZAMFARA”
Daga Taskar labarai
Wakila na musamman na Taskar labarai sun gana da wata mata a jihar Katsina da aka kama ta kuma aka sako ta bayan an biya kudin fansa.
Matar wadda Taskar labarai ta sakaya sunanta saboda tsaro ta fadawa wakilan cewa da aka kama su a motar haya sun kai su ashirin a wajen Batsari ta Katsina.
Sai aka dauke su aka yi wani daji da su can cikin wani wuri da aka ce masu dajin jihar Kaduna ne daga nan aka dawo dasu wani daji da aka ce cikin jihar Zamfara ne. Tace kowannensu sai da aka daure masa fuska yadda bai sanin ina ake tafiya bisa babura.
Tace a dajin da aka kai su sansani ne, na ‘yan garkuwar yawansu sun kai dubu. Da manyan makamai, kuma dukkaninsu Fulani ne, wadanda suka fito daga wurare daban daban a cikin kasar nan.
A sansanin akwai Hausawa ‘yan kadan suna rayuwa kai ka ce wata alqarya ce.
Ta ce duk mazan da aka kamo ana daure su kafa da hannu amma matan ba a daure su, matan da aka kamo su ne ke aikin dafa abinci da sauran hidima.
Matar ta ce sun zauna tare da ‘yan tagwayen nan na Zamfara da aka sace, tace a can ta baro su da aka sako ta ranar daren Laraba 7/11/2018. Hassana da Husaina na cikin masu aikin abinci a sansanin.
Matar tace basa cutar da mata ko ci masu mutumci, sai dai suce basu sakin matan sai an biya kudin fansa, tace a sansanin akwai mutane da yawa da aka sato kuma Kullum karo wasu a ke yi, ana saki ana karo wasu kammammun.
Matar tace sun fi azabtar da Bahaushe in sun kama shi musamman in zai yi masu taurin kai, suna cutar da Bahaushe da gayya, matar ta ce wasu kammammun na mutuwa ko domin rashin lafiya ko hawan jini, ko wata cuta ta kama su ba magani ko cin abinci da basu saba ba.
Tace in mutum ya mutu sai dai suja gawarsa su jefar a gefe ta rube da lalacewa, matar tace duk wanda aka biya kudinsa, za su kawo shi inda zai iya isa ga ‘yan uwansa kamar yadda akayi mata.
Ta bayyana cewa a sansanin babu yunwa akwai abinci na ci karka mutu.
Taskar labarai ta samu matar cikin danginta ana mata barka da wannan dowawa daga sansanin rayuwar kunci ko mutuwar walakanci.