SIYASA TA FARA FARAKKA ‘YAN KANNYWOOD

0

▼ Hide quoted text

SIYASA TA FARA FARAKKA ‘YAN KANNYWOOD

Ziyarar ‘Yan Fim ga Buhari ta raba kan ‘yan Kannywood.

 

 

-Babu Abin da Buhari ya yi wa ‘Yan Fim -Mika’il Gidigo .

Daga ISAH BAWA DORO

 

 

 

A ranar Alhamis, 18 ga watan Oktoba 2018 wasu daga cikin jaruman Finafinan Hausa da mawaka suka kai ziyara ta musamman a fadar shugaban kasa Nijeriya Muhammad Buhari domin tattauna wasu muhimman abubuwa game da harkar fim. Sai dai da alama ziyarar ta su ta bar baya da kura saboda irin yadda aka rika ce-ce-ku-ce game da ziyarar, ya yin da wasu ke ganin cewa an ware su tafiyar, an tafi da wadanda ba su dace ba. Akwai ma wasu wadanda suka bayyana cewa su ba su san da tafiyar ba sai dai kawai suka ga hotuna a soshiya midiya amma kuma an je ana  bayyanawa shugaban kasa duk ‘yan Kannywood suna goyon bayan sa.

 

 

Wata Majiya ta tabbatar mana da cewa duk ‘yan fim da mawaka da suka halarci wurin sai da aka ba kowa Naira Dubu 250, a gefe guda kuma wata majiyar ta ce naira dubu 150 ne aka ba kowa, wasu kuwa cewa su ka yi ai kishin dankali aka yi wurin rabon kudin don a akwai ma wadanda dubu 10 ma suka samu a tafiyar, tuni dai an ce wasu daga cikin su suka kama Otal a Abuja, suka ci wani abu daga kudin, an ce akwai ma wani Jarumin da sai da ya cinye kudin sannan ya baro garin.

 

 

A bangare guda kuma wasu daga cikin ‘yan fim da mawaka na Jihar Katsina sun yi wa ziyarar tofin Allah tsine! A cewar su duk wanda ya yi magana da yawun su Allah ya isa ba su yafe ba domin an maida su saniyar ware. Wanda a ganin su a matsayin su na ‘yan fim wanda suke a Jihar shugaban kasa amma su aka maida koma baya a tafiyar.

 

 

Wani Daraktan Finafinan Hausa da ba a yi tafiyar da shi ba, yana shirin kwance masu zane a kasuwa nan bada dadewa ba, a cewar sa taron maroka ne da ‘yan maula, a gefe guda kuma wata majiya ta tabbatar mana da cewa akwai wani jarumi dan Jos da ya tada rigima a Hotel kafin a raba kudi.

 

 

A bincika da Mujallar Fim ta yi ta gano akwai wasu daga cikin jaruman Finafinan Hausa da su ka ce, za su fito su bayyanawa duniya cewa su ba tafiyar Buhari suke yi ba, wadanda suka je kawai sun ari bakinsu ne sun ci masu albasa har ma suka danganta waccan tafiyar da cewa tafiyar ta maroka ce da kuma ‘yan Maula. A cikin satin da suka kai ziyarar, sai da ya zamo duk wani gungun ‘yan fim da kuma majalissar da suke taruwa babu maganar da za ka ji ana yi sai ta wannan ziyarar, har sai da ta kai ma sun fara zolayar junan su, wanda da dan fim ya ga dan fim dan uwansa sai ya ce masa ya Villa? ko kuma a ce zo ka bamu kason mu,  ko da kuwa an san ba da shi aka yi tafiyar ba, don kawai a tada zancen a ji mabambantan ra’ayi.

 

 

Maganar da aka fi tadata ita ce jawabin da jarumi Nura Hussain ya yi, wanda a cikin jawabin na sa yace, zaben 2019 ko za a danne su a yanka za su sake dangwalawa Buhari, wanda wasu daga cikin ‘yan fim suke ganin maganar tasa kwata-kwata ma ta fita daga mizanin hankali kawai ya yi ne don ra’ayin sa.

 

 

Maryam Aliyu ‘Yar Fim wadda aka fi sani da Madam Korede tana daya daga cikin jarumai mata da suka fara sukan ‘yan fim dangane da tafiyar, a wani sakon bidiyo da jarumar  ta wallafa a shafinta na Instagram ta bayyana cewa ‘yan fim din da suka je wurin shugaban kasa sun zubar masu da mutuncin, mutumin da ya hana a yi masu Film Village amma yau shi ne suke taruwa su je wurinsa, a bayanin na ta ta ce ta tabbata da ‘yan fim din kudu sai sun nuna kishin su a kan abun, amma su ‘yan Hausa fim da yake kwadayi ya yi masu yawa shi ya sa ba su da ra’ayin kan su.

 

 

Shugaban hukumar tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na’Abba (Afakallahu) yana daya daga cikin wadanda suka yi jagorancin a tafiyar, ya bayyanawa Mujallar fim makasudin ziyarar ta su, sannan kuma ya tofa albarkacin bakinsa game da irin tsegumummukan da aka yi bayan tafiyar ta su wadda ake tunanin sun samo makudan kudi jagororin tafiyar sun sanya cikin babbar riga. A cewar Afakallahu, ita masana’antar fim idan ka dauketa kamar gidan soja ne. A gidan soja za ka samu Bahaushe, za ka samu bayarebe da kuma Inyamuri da sauran su, amma daga lokacin da kowane ya  cire kakin sa shi ke Nan ya zama mai ra’ayin kan sa.

 

 

 

A lokacin da shugaban kasar Nijeriya Muhammad Buhari ya nemi da mu tara  masu ra’ayinsa a cikin masana’antar fim domin ganawa da su, babu yadda za a yi a kwaso duka ‘yan fim a yi tafiyar da su. Amma daman shi shugabanci, wanda ya samu an yi masa daidai wanda bai samu ba kuma ba a yi masa daidai ba. Amma abin da na ke so a gane shi ne; shin wadanda su ka je za su iya wakiltar al’umma da suka je sun cancanta su yi wakilcin, shin ko zuwa mu ka yi ne don kawai a cika mana aljihun mu? Duk abin da muka tattauna, mun tattauna ne a kan abin da masana’antar ta ke ciki ne. Mun yi magana a kan makaranta saboda yadda za a taimakawa jaruman mu su samu ilimi a harkar, sannan mun yi magana a kan yadda mu ma za mu rika yin Babban Production kamar yadda sauran masu sana’ar fim na duniya suke yi, mun yi magana yadda za a yi mana manyan sutudiyo na shirya Finafinai da manyan manyan kyamarori.

See also  OYO| Jima'an Amotekun Sun Kashe Fulani 7 A Ibarapa

 

 

Sannan mun yi magana a kan yadda yadda za a gyara kasuwancin harkar, ta hanyar farfado tare da gyara mana sinimomi da tiyatoci. Wadannan abubuwa guda uku su ne muka gabatar a ziyarar mu wurin shugaban kasa. Maganar mun ware wasu jihohi ka sani babu yadda za yi kowa a yi tafiyar nan da shi. A Katsina mun je da Abdu Boda da Baban Chinedu, dukkanin su mawaka ne kuma ‘yan fim ne. Babu yadda za a yi a gamsar da kowa, ba mun yi ba ne don wadancan wadanda ba a yi tafiyar da su ba ana nuna masu ba su kai ba ita siyasa ra’ayi ce. Don haka da mutum ya fito ya ce bai yin Buhari ba mu isa mu hana kowa bayyana ra’ayin sa ba.

 

 

Ita kuwa Hajiya Binta Kofar Soro wadda tana daya daga cikin jiga-jigan ‘yan fim a Jihar Katsina ta bayyanawa Mujallar Fim cewa ita masana’antar Hausa fim ta koma wa ka sani, wa ya sanka. Don haka wancan wanda ka sani shi ne zai kirawoka idan wani abun karuwa ya samu.  Mu kuwa ‘yan fim na Jihar Katsina ba mu da kowa sai Allah ba mu dogara da kowa ba, waccan tafiyar da aka yi ta ganin shugaban kasa ba mu san da ita ba, kuma babu wanda aka kirawo aka gaya mawa. Amma ina tunanin kila da sun ga ba mu kai ba, ko kuma ba mu iya kaiwa shi ya sa su ka maidamu saniyar ware.

 

 

 

Shi kuwa Fitaccen Jarumi kuma Darkatan Finafinan Hausa  Mika’il Isah Ibn Hassan (Gidigo) cewa ya yi duk ‘yan fim din da su ka je ziyarar ba masu kishin harkar ba ne masu kishin aljihun su ne, inda ya ce babu abin da gwamnatin Buhari ta tsinanawa ‘yan fim da shi.

 

 

A cewar sa, Masana’antar fim ta Kannywood tamkar katuwar rumfa ce wadda kowa zai iya zuwa cikinta misali; mai sayar da yalo, da mai sayar da makani da sauran su kowa zai iya baza hajarsa ya kuma kasa abin da ya kawo. Babban rashin adalci ne ace ku tashi ku 10 ko kuma ku 50 ko 100 ku wakilci masana’antar da ta ke da sama da mutum miliyan daya a arewancin Nijeriya. Wadancan sun je sun cewa Buhari shi suke yi, mu kuma ra’yin mu ba mu yin Buhari Tsohon Maitamakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasar Nijeriya a tutar jam’iyya PDP shi mu ke yi.

 

 

A wancan zaben gaba daya Buhari muka zaba saboda muna tunanin za a inganta tattalin arzikin kasar mu da kuma na sana’ar mu. Na tabbata a wancan zaben mun bada gudummuwa, mawaka irin su Dauda Kahutu (Rarara) Abubakar Sani, wakokin su sun taimaka wurin samun nasarar zaben shi. To, tambaya daya zan yi, waccan gudummuwa da muka bayar, me Buhari ya yi mana a Kannywood? An ce za a yi FIM VILLAGE a Kano Amma gwamnatin Buhari ta ce wannan abu ma baya daga cikin Budget gaba daya. To, idan har gwamnatin Buhari ba ta yi mana komai ba, ba ta taimaka wajen kare mutuncin sana’ar mu ba, to ka gaya mani dalilin da yasa zan sake zabar ta. A cikin wannan gwamnatin ce sana’ar mu ta durkushe.

 

 

Na yi tunanin za su ce masa mun yi ka a baya ba ka yi mana komai ba, yanzu me za ka yi mana idan mun sake zabarka? saboda ita siyasa ai kasuwar bukatace ba addini ba ce, amma abin kunya ku je kuna fadin za ku dangwala masa ko da jininku ne, wannan abin kunya ne. Me ya hana ku tambayar sa irin ci gaban da zai kawo mana, kamar yadda mu da za mu yi Atiku za mu tambaye shi abin da za ya yi wa sana’ar mu idan ya ci shugaban kasa. To, ni dai abin da zan fada duk wanda ya je taron kan sa ya ke so ba sana’ar ba.

 

 

Mutane da dama dai sun yi mamaki da ba su ga jarumi Ali Nuhu a ziyarar ba, ko da yake tuni wasu daga cikin masu sharhi tare da bibiyar al’murran da suke faruwa a masana’antar Finafinan Hausa suka bayyana Jarumin a matsayin wanda bai cusa kan sa a siyasa don kare mutuncin sa da kuma na sana’ar sa. Da Mujallar Fim ta tambayi Ali Nuhu dalilin da ya sa ba a gan shi ba sai ya ce: E, gaskiya an sanar da shi ziyarar, amma a lokacin yana Legas shi ya sa ba samu damar zuwa ba.

 

 

A yanzu haka dai za a iya cewa siyasa ta farraka kawunan ‘yan fim na Kannywood, domin wasu daga  cikin jaruman Kannywood sun fara fitowa fili suna bayyana ra’ayin na goyon bayan jam’iyya PDP a shafukan su na sada zumunta tun bayan dawowa daga waccan ziyarar ta ‘yan ga Buhari, tuni da wasu daga cikin su sun fara dora hoton Dan takarar Shugaban Kasa a tutar jam’iyyar PDP wato Atiku Abubakar, daga cikin ‘yan fim magoya bayan PDP da Atiku sun hada da: Mika’il Isah Ibn Hassan (Gidigo) Faty Muhammad, Sani Danja, Maryam Booth, Abba El Mustapha, Tamim Yusuf (Shaba)  Hafizu Bello, Alhaji Shehe, Madam Korede, Isah A. Isah, Usman Mu’azu.

 

 

Kadan daga cikin ‘yan fim da mawaka da suka yi ziyarar Buhari sun hada da: Adam A. Zango, Ali Jita, Naziru M Ahmad,  Baban Chinedu, Lawan Ahmad, Rabi’u Rikadawa, Rabi’u Daushe, Hamisu Lamido (Iyantama), Isma’il Na’Abba (Afakallahu), Dauda Kahutu Rarara, Sadi Sidi Sharifai, Aminu Alan Waka, Aminu Afandaj, Abdul Amart, Nura Hussain, Ibrahim Yala, Shehu Ajilo, Sadik N Mafiya, Elmu’az Birniwa, Shehu Ajilo, Aminu Saira, Halima Atete, Samira Ahmad, Fati Shu’uma, Rukayya Dawayya, Rashida Mai Sa’a, Hadiza Kabara, Fati Nijar, Zuby Mu’azu, Hannatu Bashir, da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here