Ya Kashe Mahaifiyarsa, Ya Kwanta da Gawarta

0

Ya Kashe Mahaifiyarsa, Ya Kwanta da Gawarta

 

Samuel Akpobome Emobor matashi dan shekara goma sha takwas mazaunin gundumar Ologbo a Karamar hukumar Ikpoba-Okha a Jihar Delta, ana zarginsa da kashe Mahaifiyarsa sannan kuma ya kwanta da gawarta, saboda ya yi kudi.

 

An gabatar da Samuel a Babbar hedikwatar Yansanda ta jihar Edo ga manema labarai in da Ya fada ma su yadda wani boka mai sayar da magunguna ya zuga shi ya aikata wannan mummunar laifi.

 

Kamar yadda ya fada ya bayyana cewa ” Na so yin amfani da mahafiyata ne domin in yi tsafi in samu kudi, ni shekaru na goma sha takwas, mahaifina ya rasu. Akwai wani mutum mai suna One Love shi ya sanar da ni cewa in yi tsafi da mahaifiyata domin in yi kudi.

 

Ya yi man alkawarin zai ban Naira dubu Hamsin in na kashe Mahaifiyata kuma na kwana da ita, sannan ya ce in cire idon ta da yatsunta in kawo mashi. Na so na cire idon da yatsun kafin mutane su zo, sannan na kwanta da ita sau daya, na kashe ta ne a lokacin da take bacci. One Love ya sanya wani abu cikin abin sha ya bani nasha, sannan ya ce na je na kashe ta.

 

Ina matukar bakin ciki, musamman ma yadda na sha bugu daga wurin mutane, bayan na aikata abin da bokan ya umurce ni.

 

Kwamishinan Yansanda na Jihar Edo Babatunde Kokuma ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce zasu mika shi kotu domin fuskantar hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here