GARKUWA DA MUTANE: KO DA SAKACIN GWAMNATI?

0

GARKUWA DA MUTANE: KO DA SAKACIN GWAMNATI?

 

~~~~~Daga wanda ya je inda suke watayawa~~~~

 

Daga Wakilin Taskar labarai

 

Da sanyin safiyar ranar 9/11/2018 muka dunguma zuwa wata gaisuwa ta mahaifin wani almajiri da ya zama dan gida a gidanmu, bayan aiko masa da aka yi na cewar barayin shanu sun hallaka mahaifinsa a wani kauyen Zamfara, sannan su jikkata kanin maaifin na sa, kuma sun tafi da wasu kannensa guda biyu, ‘yayan kanen mahaifinsa da niyyar sai an asu kudin fansa su sako su.

 

Ba zan bayar da labarin dalilin kashe Mahaifin nasa ba ko kuma dalilin yin garkuwa da kannen nasa, zan tafi kai tsaye ne kan abubuwan da suka faru a yayin tafiyar.

 

Tun tashin farko ma an kai ruwa rana kafin a gidanmu a amince man in yi tafiyar, amma na cije da cewar ba kome sai na je. Bayan an hakura aka yi ma na addu’a muka tafi ni da Umar wanda ya ke shi ne aka yi wa rasuwar.

 

Bayan mun wuce Wani gari mai suna Illela da ke karamar hukumar Batsari, tun daga nan aka fara jajanta mana kan bai kamata mu yi wannan tafiyar ba kasancewata bako, duk da cewa akwai yan garin da suje zurgazurga da mashin zuwa garun da zamu mai suna Shamushalle.

 

Haka dai a cije aka yi mana goyan biyi ni da Umar da dakakkiyar zucyata muka nufi wani Qauye da ake kira Dagwarwa wanda shi ne iyaka tsakanin Katsina da Zamfara, ko a wannan kauyen kadai ka tsaya zaka tabbatar cewa ka fara shi ga wata nahiya da yaki ya daidaita, musamman yadda da yawa mutanen garin sun tashi saboda yadda garin ke cikin daji.

 

Gaba na bai fara faduwa ba sai da muka bar garin muka nufi Shamushalle sannan fa ido na ya fara rena fata, a lokacin da na fara ganin jefi-jefin mutane da kakain sojoji bisa mashin a cikin dajin.

 

Mai mashin din da ya dauko mu ya sanar da ni cewa wadannan mutanen fa da nake gani duk Barayi ne ba sojoji ba ne, kuma in suka ga bakuwar fuska kome na iya faruwa. Hantata ta kada nadama ta fara zuwan mani, na rasa me zan fada masa ma sai dai na yi shiru na cigaba da addu’o’i a zuciyata, Umar ne ya kara man kwarin guiwa da cewar ai akwai amana tsakaninsu, ko da an taremu ba abin da zai faru in Allah ya yarda in har sun sanar da su.

See also  UMAR FAROUQ ADVOCATES STRENGTHENING OF ORGANIZATIONAL STRUCTURE, SEVICE DELIVERY, IN HUMANITARIAN MINISTRY 

 

A haka muka cigaba da tafiya ba tare da na yi koda tari mai karfi ba. Har muka kai wata mararrba wadda daga nan bai fi kilomita biyu a zuwa cikin garin Shamushalle. A nan wani mai mashin dauke da wasu ‘yan garin ya fito ya tsayar da mu, bayan yi yiwa Umar Gaisuwa sai ya ke sanar da shi cewa a shawara ni kamata ya yi in koma daga nan domin tabbas in na shiga garin suka lura ni bako ne ko an ce ga inda na zo komemna iya faruwa, fitsari ya neme ya kufce man bayan da na hangi wata tawagar mashina dauke da mutane masu kayan sojoji da kuma bindigu rataye a kafadinsu, sun yi hanyar garin. Na ci gaba da salallami ciki na na kadawa ina ta raba idanu tsakanin mutanen da ke labarin.

 

A wannan tsayuwar da muka yi mun ga wadannan filani masu sanye da kayan sojoji sun fi a kirga suna wucewa kuma duk dauke da bindigu, abin da zai rabe masu da sojojin gaske shi ne takalman roba da suke sanye da shi, da kuma yawa da wandon ya yi wa wasunsu.

 

A haka Umar ya ce in juyo kawai shi zai karasa gida, na sauka na hawo mashin din da ya bamu shawarar in koma, ya kasance mu hudu ke nan bisa mashin din aka sanya ni tsakiya direban ya tayar ya nufo Batsari, ni kuma ba abin da na ke sai salallami da zufa.

 

A haka cikin ikon Allah ba tare da wata matsala ba muka iso Batsari. Hankali na ya dawo jiki na, a inda muka tsaya sai da na sha ledar ruwa uku, duk ban san daliliba.

 

Abubuwan da na lura da su a wannan tafiyar kusan duk tambayoyi ne kamar haka:

 

Su wa ke baiwa wadannan filani Kayan sojojin da suke sawa?

 

Me ya sa mutane ke yadda su kulla amana da marasa amana

 

Me yasa yanzu sama da wata tara babu jami’an Yansanda a garin Shamushalle saboda barayi da suka yi sansanin garin

 

Shin Gwamnatin Zamfara ba ta san da irin wadannan garuruwa ba ne, da ta bar barayi na cin karensu babu babbaka? Har ta kai ga cewa su ke hukunci a yanzu, kuma wurinsu ake kai kara.

 

Daga karshe muna kira ga Mahukunta da su kai dauki yankin Shamushalle, domin nan ma babban sansanin mabarnata ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here