HADUWA TA DA MASU GARKUWA DA MUTANE

0

HADUWA TA DA MASU GARKUWA DA MUTANE

 

“Labarin wani mutum”

 

Daga Taskar labarai

 

Wakilan Taskar labarai na musamman sun zanta da wani mutum da muka sakaya sunansa saboda dalilai na tsaron lafiyarsa, da ya ba da bayanin yadda ya taba haduwa da masu garkuwa da mutane a daji Inda yace,

 

“Sana’ata shi ne yin itace a daji in kawo gari in sayar, wata rana a daji na gama itace ina daurewa a baro sai kawai naga mutane da bindigogi sun sa ni tsakiya, suka ce mani “me za su samu?”

 

Nace masu ni yunwa ma na ke ji kuma bani da komai,

sai suka ce to, bar itace ka biyo mu nace to na bi su mu ka yi ta tafiya cikin daji duk da bindiga ni ko kara babu a hannuna.

 

Bayan tafiya mai tsawo a daji sai muka iso wani sansani su, gasu nan mata da maza yara da manya. Sai aka ce in zauna gindin wata bushiya aka kawo mani soyayyen nama mai yawa a kwano da lemun roba da kuma ruwa na leda, naci na koshi. Suka barni zaune tsawon wasu awowin ba wanda yace man kanzil. Can suka ce, zan iya gane hanya nace kila suka ce wani yaro ya raka ni yaron ya dauko bindiga ya rataya ya ce mu tafi.

See also  Kotu Ta Daure Dan Damfara Shekara 235 A Kurkuku

 

Zamu tafi sai Daya yace gobe in za ka zo ka sawo mana Tiramol ka kawo mana sai nace wallahi banda kudin Tiramol, sai suka ce nawa nake samu ribar itacen Inna sayar? Nace naira dari biyar.

 

Su ka ce wawa sakarai don dari biyar kake wannan wahalar? Su ka yi ta zagina suna ce man mawahalci, sai suka dauko naira dubu suka bani sukace gobe in an shigo itace in zo masu da Tiramol.

 

Wanshekare da nazo Inda nake itacen na iske daya daga cikin su yana jira na, ya miko hannu na dauko sakonsu na ba shi ya juya, ya shiga daji, ni kuma na yi itace na na dawo cikin gari..

 

Wannan ya faru kamar wata daya da ya gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here