AN SACE WASU MATA TSAFFI A YANKIN BATSARI

0

AN SACE WASU MATA TSAFFI A YANKIN BATSARI

 

Daga Taskar labarai

 

Wakilan Taskar labarai na musamman sun tabbatar da satar wasu mata tsaffi a yankuna daban-daban na karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

 

Matan an sace su, watakila don ‘ya’yansu su kawo kudin fansa, kamar yadda binciken Taskar labarai ya ke hasashe.

Matan akwai mahaifiyar wani dan kasuwa mai suna Alhaji Tanimu dake wani kauye !ai suna Kauran Gero, matar mai suna Fatima an sace ta lokacin dan nata yana Anaca wajen kasuwancinsa.

 

Wata matar da aka sace ita ce, Aisha mahaifiyar wani dan kasuwa mazaunin Kano mai suna Alhaji Basiru daga wani kauyen Kokiya, attajirin an ce ya yi kokarin maida mahaifiyar tasa Kano amma taki yadda har yanzu da wannan, mummunan al’amari da ya faru.

 

Haka kuma, an sace mahaifiyar wani mai suna Alhaji Isa dake wata Ruga a yankin Kimbitsawa matar mai suna Hasiya mai kimanin shekaru saba’in a duniya.

 

Kazalika, an sace wani mutum mai suna Alhaji Atti wanda yake kauyen Doga a karamar hukumar safana.

 

Dukkanin​ wadanda aka sacen babu wata magana, daga wadanda suka sace su, dama Al’adarsu barayin na mutane shi/ne in sun dauke mutum sukan dauki dan lokaci kafin su tuntuba.

 

Taskar labarai bata samu wani bayanin ‘yan sanda ba a kan wadannan sace-sacen na mutane na baya-bayan nan a karamar hukumar ta Batsari a jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here