SHARI’AR TSOHON GWAMNAN JIHAR KATSINA IBRAHIM SHEMA AN SHIGA MATAKIN SHARI’A CIKIN SHARI’A

0

SHARI’AR TSOHON GWAMNAN JIHAR KATSINA IBRAHIM SHEMA AN SHIGA MATAKIN SHARI’A CIKIN SHARI’A

 

A yau litinin 12/11/2018 aka dawo zaman kotu wanda ake tuhumar tsohon gwamanan jihar Katsina Bar. Ibrahim Shehu Shema da wasu Mutane uku kan sama da fadi da wasu kudaden kananan hukumomi da yawansu ya kai Biliyan Sha daya (11bn).

 

Bayan alkali ya shigo sai ya fara karanta matsayar kotu kan amsar wasu takardu na shedu da Lauyoyin EFCC suka gabatar, in da alkalin ya amita da takardu ukun da aka gabatar a matsayin shedun, akasin da Lauyoyin Shema suka kalubalanta a zaman da ya gabata.

 

In da alkalin ya bayyana cewa takardun duk an samo su ne daga bankuna in da ake zargin na aka karkatar da kudaden.

 

Daya daga Lauyan EFCC ya bayyana cewa, wanda ake zargi na uku shi ya dauki bayanansa da kansa kuma hannunsa ya rubuta ba tirsasashi ka yi ba. Haka ma wanda ake zargi na hudu shi ma shi ya rubuta jawabin da kansa ba tursashi aka yi ba, sannan ya sanya hannu sau uku yana rubuta jawabinsa da kansa.

 

Bayan lauyoyin wadanda ake tuhumar sun amshi takardun bayanan sun gana da wadanda ake tuhumar sai, sai suka dawo, Lauyoyin wadanda ake tuhumar sun bayyana cewa ba su amine da takardun ba domin kuwa tilasta wadanda ake tuhumar aka yi suka rubuta bayanan, inda suka bukaci alkali ya basu dama a yi shari’a cikin shari’a domin su kalubalanci wadannan shedu.

 

Alkali ya amincewa lauyoyin wadanda ake tuhuma na fara shari’a cikin shari’a, in za a yi shari’a EFCC su tabbatar wa kotu cewa ba tilasta wadanda ake zargi aka yi ba suka rubuta bayanan, su kuma wadanda ake zargi su kare kansu da cewar tilasta ma su aka yi.

 

Alkali ya dage shari’ar zuwa ranar 28/11/2018 domin cigaba da sauraren karar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here