SHUGABAR HUKUMAR TASHOSHIN JIRAGEN RUWA TA SHA ALAWASHIN MAKA JARIDAR SAHARA REPORTERS KOTU.

0

SHUGABAR HUKUMAR TASHOSHIN JIRAGEN RUWA TA SHA ALAWASHIN MAKA JARIDAR SAHARA REPORTERS KOTU.

 

A wata takarda da shugabar hukumar tashoshin Jiragen Ruwa Hajiya Hadiza Bala Usman ta raba wa manema labarai, ta karyata zargin da Jaridar Sahara Reporters suka fitar na zargin ta da Bayar da cin Hancin Dala miliyan Biyu domin Uba Sani ya samu takarar Kujerar Sanata Na Kaduna ta tsakiya.

 

Kamar yadda rahoton na Jaridar ya bayyana Hadiza Bala Usman ta mika Dala miliyan biyu ga Faruk Adamu domin a tabbatar da Uba Sani kujerar Sanata.

 

Hadiza ta bayyana cewa, wannan rahoton baki dayansa karya ne, kuma zubar da kimar da aka san aikin jarida na da shi ne, musamman yadda ake girmama kafafen yada labarai a wannan kasar. Ta bayyana cewa ba za a taba zato gidan Jarida kamar Sahara Reporters wanda ya kamata ya kare martabarsa da ta jama’ar kasa, amma a same shi ya na yada labaran kanzon gurege ba da bata kimar wasu a kasa.

See also  'Yan Arewa Mu Farka, Kar Mu Bari A Sake Yi Mana Sakiyar Da Ba Ruwa - Alhaji Ibrahim Galadanci

 

Hadaiza ta Bayyana cewa ta ba gidan Jaridar Sahara Reporters kwana bakwai su bayyana hujjarsu na wannan labari ko kuma ta dauki matakin Shari’a da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here