BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN JAMIYYA NA KASA ADAMS OSHIOMOL

0

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN JAMIYYA NA KASA ADAMS OSHIOMOLE.

 

Sakamakon zabukan share fage na Jamiyyar APC da aka gudanar ya nuna cewa Engr Yakubu Danja ya lashe zaben da kuri’u 314 inda abokin takararashi kuma Dan Majalissa mai ci Amiruddeen Tukur Bakori ya ci kuriu 305.

 

Zaben na Dan Majalissar Wakillai ta Tarayya ya samu sheda ta san hannun yadda da zaben ya gudana kamar ka:

 

1. Wakillan Yan Takarar guda biyu sun aminta da haka sun sa hannu duka kowa ya yarda. An kuma bayar da kwafin sakamakon ga dukkan wakillan biyu.

 

2. Takardar yarda da aminchewa da sakamakon wanda aka yi a gabansu suka sa hannu mutanen sun hada da;

A. Shuwagabannin Yan Sanda (DPOs) na kananan hukumomin Bakori da Danja.

B. Shuwagabannin Yan Sandan ciki (SSS) na kananan hukumonin biyu.

C. Shuwagabannin Civil Defence na Kananan Hukumomin

D. Turawan zabe watau Electoral Officers na Bakori da Danja.

 

3. Sakamakon zaben na Jihar Katsina wanda ke dauke da sa hannu Dr. isah Adamu ya nuna sunan Engr Yakubu Nuhu Danja ne ya lashe zaben.

INA MATSALAR TAKE?

Bayan kammalawa da gabatar da sakamakon zuwa Hedikwatar Jammaiya a Abuja sai aka chanza sunanshi da wanda ya kada . Ana zargin Amiru Tukur Bakori ya bayar da makudan kudade domin tabbatar da yin haka. Daga cikin wadanda ake zarge da karbar na goro sun hada da Shugaban jamiyyar na kasa, National Organising Secretary da kuma Administrative Secretary.

Har inda muke yau duk kokarin da za a yi na ganin mai gaskiya ya mashi abunshi, abun ya gagara.

 

RAWAR JAMIYYA TA JIHA

A nan matakin Jiha, Jamiyya ta rubuta ma Headquarter APC takardar koken rashin gaskiyar da aka yi ta yi kira da a gyara. Inda aka yi kwafin wannan takardar ga Mai Girma Gwamna da Shugaban Kasa.

 

Kwararun hujja ta sheda mamu cewa Shugaban Kasa ya ummurci Shugaban Jamiyya na Kasa da gyara wannan rashin adalci amma yayi kunne uwar shegu da shi. Daga bisani ya tsallake zuwa kasar Amurika don Dino Mai Dakinshi da ba ta da lafiya.

 

Ya zama wajibi a nan don yin wannan bayani a wannan kafa domin yin kokarin fidda jaki daga duma.

 

Idan za a iya tunawa irin wannan wasa da hakki ba ya cikin tari da manufar wannan jamiyya hasali ma kokarin kamanta gaskiya da adalci ne ya kawo ta bisa wannan mulki.

 

Da fatan Allah ya fiddo mashi hakkinshi.

 

Kabir Umar

07034610481

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here