Majalisar Sarakuna ta nuna damuwa kan Ilumin yara a Arewa
Daga Zubairu T M Lawal Lafia
Majalisar Sarakunan gargajiya na qasa yankin Arewa ta kafa kwamitin da zai yi aiki kan farfado da ilumin yara a Arewacin Nijeriya.
Miliyoyin yarane kefama da qarancin Ilumi a qasan nan masamman vangaren Arewacin Nijeriya Majalisar Sarakunan ta bayyana hakane a zaman taron kwanaki biyu da ta gabatar a garin Kaduna ranakun 10-11 ga watan da yagabata.
Hukumar kula da yara marasa galihu ta Duniya wato (UNICEF tare da cibiyar Sultan ta wanzar da zaman Lafiya da cibiyar bayarda Ilumin bai daya UBEC sun yaba tare da nuna goyon baya ga wanan shirin na tallafawa yara qanana da ilumi. Saboda Ilumi shine kadai abinda zakaba yaro ka taimakawa rayuwarsa a yanzu yadda Duniya take tafiya a tafarkin Ilumi an kawar da jahilci.
Taron da ya kunshe Sarakunan Gargajiya na yankin Arewa da Dattawa masu fada aji sun nuna damawa da wanan matsalar dake addabar alumman Arewa , Wanda rashin samun Ilumi ga rayuwar yara babban matsalane ga rayuwan qasa baki daya .
Da yake jawabi Maimartaba Sarkin Musulmai Alhaji Sa’ad Abubakar Sultan na Sokoto ya bayyana cewa wanan matsalar tafi addabar yankin Arewa Maso gabas da Arewa Yammaci inda yara ki fuskantar kalu balaen rashin zuwa makarantu sakamakon rigingimun dake adabar yankunan.
Yace; zamu tabbatar da kwamitin da za’a nada ta dauki kwararan matakai wajen magance wanan babban kalubalen wanda idan aka barshi bazai haifar ga xa mai idoba nan gaba.
Matakinnan zai shafi yara dake rayuwa masamman a yan kunan karkara. Sanan zasu samar da hanyoyin tallata wanan shirin na taimakawa yara su samu ilumi , ta vangaren Malamai da Shugabannin qabilun da jagororin alumma masamman na karkara.
A kididiga na ma’aikatan Ilumi ta qasa ta bayyana yawan yara kimanin 10.5 miliyon ne ke fuskantar wanan matsalar rashin ingantaciyar ilumi. Masamman yara daga shekara 6 zuwa 14 yace kashe 45 cikin wadanda ke fuskantar wanan matsalar na rashin karatu a nahiyarmu yara matane.
Rashin ilumi babban matsalace ga harkan tattalin arziki a qasa kowace irice. Harkokin shari’a sun bayyana kasafi ko kudaden shiga yana samun tagomashine daga harkan Ilumi da cigabanku . Idan ya zama babu Ilumi babu cigaba talauci zai mamaye rayuwarku Ku zama cima baya .
Da Ilumi ne ake samun cigaba ta hanyar kimiyya da fasaha da sanin abubuwan cigaban rayuwa saya da saidawa.