MDD zata hada hannu da Shugabanni wajen taimakawa jama’an Arewa maso gabashin Najeriya

0

MDD zata hada hannu da Shugabanni wajen taimakawa jama’an Arewa maso gabashin Najeriya

Daga Zubairu Muhammad

A watan Oktoba da ya gabata ne Shugabannin sashin Majaisar Dinkin Duniya da ke kula da ci gaban Qasashe, wato UNDP Achim Steiner da kuma mai kula da sashen bayar da taimakon gaggawa, Mark Lowcock, suka yi kira ga kungiyoyi dake Qasashe da kuma na qasa da qasa da su hada karfi da karfe domin taimakawa yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Yankunan da suka hada Barno, Adamawa da Yobe. A lokaci guda kuma za su inganta samar da ayyukan yi cikin gaggawa. Ga alumman yankin wadanda Rigingimum Boko Haram ya shafa .

Hukumar tace sama da mutum miliyon 7.7 ne suke fama da matsanaci rayuwa a sashin Najeriya mafi yawansu suna yankin Arewa maso gabas ne.

Hukumar ta kuduri aniyar taimakawa wadanda suke bukatar taimako na jinkai domin sake gudanar da rayuwar su . a ziyarar da manyam mukarabai na Ofishin Majalisar Dinkin Duniya ta kawo inda ta samu zantawa da wasu kusoshi cikin Gwamnatin Nijeriya ciki harda Ministan kudi Hajiya Zainab Ahmad yayin ziyarar a tattauna ayyukan jinkai da za’a fara gudanarwa a garin Bama da Ngwom dake jihar Borno .

Shirye shiryen abubuwan da za’a taimaka masu dashi zai hada da koyar dasu qananan sana’o’in hannu wanda zai taimakawa rayuwarsu na yau da kullum .

Da fadada hanyoyin cigaba da kula da rayuwar marasa galihu da qananan yara, Mr. Lowcock, yace; zamu hada karfi da karfe da Gwamnatin qasa da masu fada aji domin taimakawa wadanda ire-iren wanan iftila’in ya shafa masamman yankin Arewa maso gabashin Najeriya. Wanan ya sanya kungiyar dabam dabam kamar UNDP suka hada hannu domin gyara rayuwar wadannan mutanin.

See also  YA GINAWA MAHAIFIYARSHI MAKARANTA DA MASALLACI A MATSAYIN SADAKAT JARIYA

Ta hanayar koyar dasu sana’o’in hannu na za!ani da zai rage radadin talauci , kuma sana’o’in zai taimakesu ta hanyoyin gudanar da rayuwarsu da yaransu Wanda raigapimar ya daidaita.
Shima Mr. Steiner yace; dolene MU hada karfi da karfe domin dawo da rayuwar wadannan mutanin mu Samar da tsaro da zai magance rigimar da tayi taci tsawan shekaru masu yawa.

Wanan zai sanya alumman dake rayuwa cikin kunci a karkara da wadanda ke rayuwan a sansanonin gudun hijira su samu kwanciyar hankali da gudanar da sana’o’in su cikin sauki .

Yace hakan ya sanya Majalisar Dinkin Duniya ta karfafa kungiyoyi masu bada agaji manya da qanana saboda a samu hanyar taimakawa wadanda ke gudanar da irin wanan rayuwa na kunci.

Ya kara da cewa samar da tsaro da abinchi da magunguna wajibine saboda shine matakin farko da alumman ke bukata .daga nan sai koyar dasu hanyoyin dogaro da kai.yace; akwai miliyoyin yara qanana yan qasa da watanni 6 zuwa qasa da shekaru biyar rayuwarsu na bukatar taimako ko wani iri. Yace wanan aikin yana bukatar kashe biliyoyin dalolin Amurka Wanda zai agazawa wanan aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here