DAN TAKARAR GWAMNA A PDP NA NEMAN TALLAFI

0

DAN TAKARAR GWAMNA A PDP NA NEMAN TALLAFI

Daga Taskar labarai

Wani bincike na musamman da Taskar labarai ta yi ta gano dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP da mataimakinsa a jihar Katsina sun fara neman tallafi na kudi da kuma bashi Don samun kudin da za su yi yakin neman zabe da su.

Binciken ya tabbatar mana da cewa har kudin tallafin ya fara shiga hannunsu, wasu kuma da aka nemi su bayar suna neman sanin tabbacin yiyuwar cin zaben na su kafin su san ya zas u zura jiki su sanya kudin su a zaben.

Wani ya tabbatar wa da TASKAR cewa wani makusancin wani attajiri har ya !ika nasa tallafin, wani kuma daga wata jiha ya aiko Katsina a bincika ma sa, ko Dan takarar zai iya cin zaben? Idan zai iya to zai zuba jarinsa, in kuma a a zai ba da na shan ruwa lokacin yakin neman zabe kawai.

Taskar labarai ta samu tabbacin ‘yan takarar na ganawa da wasu mutane masu kudin gaske akan su zo su zuba jarinsu a ci zabe a biya su kudinsu kuma a kafa gwamnati dasu, abinda wadanda ake ma magana suke dari-dari da/shi kamar yadda binciken mu ya tabbatar.

Taskar labarai ta gano wasu jiga-jigai a PDP sun damu akan cewa basu san ya ake neman tara gudummuwar yakin neman zaben ba, kuma ya za a tafiyar da kudaden in an samu.

Neman gudummuwa ba wani abu ba ne a yakin nemanm zabe Al’ada ce ta jam’iyyu kuma halastaccen abu ne, ko a kasashen da suka ci gaba.

See also  Cire tallafin mai: Najeriya Ta Adana Trilliyan 1.45

Amma abin da ya sa ya zama labari a Katsina shi ne, ana yada cewa dan takarar PDP Yakubu Lado Danmarke yana da kudin da zai iya takara ba tare da ya nemi tallafin kowa ba, kuma wai akan naka a ka bashi takarar.

Amma sai gashi ba aje ko’ina ba, ana yawo da kokon bara da takardun yarjejeniya, wannan ya sa kowa kansa ya daure yake mamakin me ke faruwa?

Jaridar taskar labarai ta yi kokarin jin ta bakin shugaban jam’iyyar PDP Alhaji Salisu Yusufu Majigiri kuma dan takarar mataimakin gwamna amma abin yaci tura an kira wayarsa bai dauka ba an kuma tura masa sakon waya bai amsa.

A wata sabuwa Dan takarar shugaban kasa a PDP Alhaji Atiku Abubakar ya amince da kafa kwamitin da zai tafiyar masa da yakin neman zaben sa a Katsina.

Sabanin yadda Dan takarar PDP Yakubu Lado Danmarke ya nema cewa a bashi dama a matsayin sa na Dan takara gwamna a PDP ya zama ko ya kawo wadanda zasu zama ko’odinetas/na yakin neman zaben na Atiku.

Ance wasu jiga jigan PDP a tarayya suka fadawa Atiku cewa in ya yi Hakan a ko’ina a hir yace zai yi hakan a Katsina kuma Atikun ya amince har ma ya amince da zabo mutane biyar masu mutumci a cikin PDP na Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here