GWAGWARMAYAR NEMAN KUJERARA GWAMNAN KATSINA A 2023: SHIRE-SHIREN ZANA’IDAR GIDAN SIYASAR DANGIWA

0
837

GWAGWARMAYAR NEMAN KUJERARA GWAMNAN KATSINA A 2023: SHIRE-SHIREN ZANA’IDAR GIDAN SIYASAR DANGIWA

A nan jihar Katsina an yi gidajen siyasa a baya masu karfin gaske, amma a hankali zamani yayi tafiyar ruwa dasu, yanzu sai dai kufai ko Kuma Dan abinda ba a rasa ba.

 

A halin yanzu a fadin jihar Katsina kaf! Idan ka debe gidan siyasa guda daya tak, wato gidan Abu Ibrahim, to zan iya cewa babu wani gidan siyasa da yake da karfi da tasirin gidan Amadu Musa Dangiwa. Sai dai masu nazari da sharhi na ganin cewa idan ba a yi hankali ba shi ne gidan da zai kafa kyakkyawan tarihi da mummuna a hade.

 

Ya kafa tarihi a matsayin gidan da ya shahara wajen hadin kai, da jajircewa, sannan kuma mafi yawan jiga-jigan da suke tafiyar da lamurra a gidan matasa ne . Sai dai Kuma idan ba a yi hankali ba zai kafa tarihi a matsayin gidan da bai yi karko ba, ko Kuma wanda yafi kowane rashin dadewa yana tasiri, saboda dalilai kamar haka ;

 

 

• Rashin kyautatawa magoya baya ; da yawa daga cikin wadanda aka dade ana Fadi tashi da su a tafiyar gidan suna kuka ko korafin ba a kula da su a yanzu da lokacin da yakamata a yi hakan yazo, kusan duk wanda za ka tattauna da shi, karami ko babba sai ka same shi yana korafin abin.

 

Wasu tun daga 2002 suke tare da tafiyar sun bada lokuttan su, sun saka dukiyar su, sun yi amfani da basirorin su da ilimin su, wasu sun fuskanci baraza kala-kala a wurin gwamnatocin baya duk saboda tafiyar, bisa kyautata tsammanin cewa idan aka kai ga nasara zasu samu wata dama, ko dai a cikin sana’o’in su ko a ayyukan su.

 

Amma yanzu da aka samu damar, maimakon a taimake su, sai aka buge da taimakon wadansu can da basu san yanda aka yi nasarar ta samu ba. Wani da muka tattauna da shi wanda yana daya daga cikin wadanda suka bada komi na rayuwar su domin samun nasarar tafiyar gidan Dangiwa, a lokacin kare korafin da yazo man dashi a kan shi kansa maigidan namu wato Arc Ahmad Musa Dangiwa, sai yake cewa yanzu don Allah za ka iya lissafa mani daga cikin mutanen mu wadanda ya taimaka Koda mutum goma?

 

Shi ne MD na Mortgage bank suna gina gidaje a ko’ina a fadin kasar nan mutum nawa ya kai ya sa aka basu Koda kwangilar kawo yashi, ko siminti, ko rodi, ko katako ?

 

Mutum nawa yasa aka ba allocation na gidan? Mutum nawa ya kai can ko a matsayin siniya ko jiniya staff, kai Koda masinja mutane nawa ya Kai?

 

A karshe ya ce man yanzu saboda Allah zaka hada shi da Hadi Sirika? Yanzu kana iya lissafa man biyar kacal daga cikin manyan ‘yan gaba-gaban gidan Hadi wadanda bai taimaka ba? Nace a a, yace to ni sai na lissafa maka mutane dubu jiga-jigan gidan Dangiwa wadanda ko sannu har yanzu ba a yi masu ba.

 

Sannan ya sake jeho man wata tambayar yace mutum nawa kasani daga cikin manyan hadiman tafiyar gidan Ahmad Musa Dangiwa wadanda ko dai yaba mota, ko yasaya wa gida ko ya basu kujerar Makka? Nace gaskiya ban san ko daya ba, amma dai na san ba za a rasa ba, amma ka bari zan binciko.

 

Sai yace mani to ni yanzu Ina iya lissafa maka mutane dari 100 wadanda Hadi Sirika ko dai ya ba su gida, ko mota ko kujerar aikin hajji, ko ya basu kudi su kara jari daga miliyan daya zuwa kasa. Ai don Lada ake sallah Koko kana so kace shi MD din tunda aka bashi kujerar tattalin arzikin sa bai canza ba? Nace a’a dolene ya canza mana. Sai yace to idan hakane me yasa su wadanda ya taka ya kai ga kujerar ba zai taimake su ba?

 

Ai ba shi kadai aka ba kujerar ba, da shi da magoya bayansa aka ba. Irinku masu makauniyar soyayya bakwa so a fadi laifin MD da mutun yayi magana sai ku taso masa.

 

 

Nuna bangaranci da wariya ; da dai na lura ba zai taba yarda na kayar dashi ba, sai nayi kokarin juya akalar zancen, nace masa ai Amadu Babba yana yi, Kuma idan Amadu Babba ya yi kamar Dangiwa ne yayi. Ai kamar na watsa masa wuta yace “Da Allah ka yi shiru bama gara shegen kowa dana buruwa ba, duk a ciki akwai ma wanda yake son rusa gidan Dangiwa kamar sa? Mutumin da ya babu komi cikin zuciyar sa, sai bangaranci, bakasan cewa guraben ayyuka har guda 90 ya raba a karamar hukumar kankiya ba daga 2011 zuwa yanzu, Amma don tsananin kabilanci 87 duk a cikin garin kankiya ya raba su, sauran mazabu 7 da suke wajen kankiya abinda suka samu bai fi 6 ba.

 

Kai ko a cikin garin garin kankiyar ma kaso mafi tsoka a bakin kasuwa ya raba su. Nace to Amma meyasa kace shi ke son kashe gidan Dangiwan? Sai yace ai ka San yanzu shima gani yake ya kawo karfi, saboda haka nashi gidan yake so yayi, amma wannan ai zargi tunda baka da hujja nace masa.

 

Sai yace to ka zauna yanzu zan jero maka hujjoji guda akalla bakwai da suke tabbatar da haka, idan baka yarda ba sai kaje ka bincika .

 

( a) Na farko idan baka manta ba akwai wasu mutane su uku da aka bawa mukamai daga cikin ahalin gidan Dangiwa amma daga baya suka yi tawaye, nace na sani Amma ai wadannan mutanen bashi da alaka dasu. Eh kowa haka yake gani Amma ba haka abin yake ba.

 

(b) Yanzu a karmar hukumar Kankiya su wanene jiga-jigan gidan Dangiwa? Musa, Danjuma, Salisu, na fada batare da na daga kai na kalle shi ba. Yace to kaje ka bincika su duka babu wanda bai yi kokarin jijjigewa ba, ta hanyar taimakon masu adawa dasu ta bayan fage.

 

c) Kwanannan aka gama zaben Reps Kankiya, Kusada, Ingawa, Speaker da shi da wa suka yi takara a cikin APC ? Nace babu, ya sake tambaya to shi kuma Gali da shi da wa sukai zaben fidda gwani ? Nace babu, sai yace to a Kankiya Maigemu shi ma shi kadai ya yi takara a APC nace a a , yace to me yasa?

 

Nace saboda akwai masu nema, sai yace su wadancan kujerun kana nufin babu masu neman su, Koko dai hana su akayi su nema? To me hakan ke nufi ? na sake jeho Masa da tambayar da sauri.

 

Wadancan yaran sa ne wadanda a yanzu loyalty dinsu gareshi yake ba ga Dangiwa ba, saboda haka suna da matukar muhimmancin gaske wurin fara gina nasa gidan, shi kuma wannan nasa loyalty din Kai tsaye ga Dangiwa yake, shi yasa ya kawo nasa kuma da Allah yasa ya yi nasara, to da daga nan ne za a matsa ga plan B.

 

d) Kaje ka bincika ni dai nayi nawa binciken, duk wani jigo a gidan Dangiwa ko wanene bai isa yakai wani ko wasu wurin Amadu Babba yace ga wane ka taimake shi, ko Kuma yace kayi masa alfarma kaza ya yi ba, wallahi baya yi, Kuma bai taba yi ba . Nace to saboda me ? Shi yakamata ayi wa wannan tambayar.

 

Waima tukun dakata da Allah, shin menene ya kawo batun wani gidan Dangiwa, da gidan Amadu Babba, Ni dai a iya sanina babu wani gidan Amadu Babba, Kuma saboda me ma zai yi nasa gidan bayan babu wani mutum da ya ci moriyar gidan Dangiwa kamar sa?

 

Sai yace kai yanzu ba zaka fahimta ba, Amma Kaje ka rubuta ka ajiye, wallahi ana gama zaben 2019 za kaga rigingimu sun fara kunno Kai gidan Dangiwa, Kuma ni babu wanda nike tausaya mawa kamar shi Dangiwan, saboda idan bai yi hankali ba, za a yi irin abinnan da ake cewa ‘ kwace goruba a hannun kuturu….’ . To wai duk me zai kawo rigimar? Na tambayeshi.

 

Sai yace ka san da cewa ana batun idan Allah ya kaimu 2023 Daura zone za ta nemi ita ma a bata kujerar Gwamna ? Nace tabbas na ji, Kuma nima Ina cikin masu goyon bayan hakan, sai yace to a cikin yan siyasar Daura zone a ganinka su wanene masu karfin da za su iya neman kujerar Gwamna ? Su uku ne, na ce masa, dawa-dawa ? Na ce da Amadu Dangiwa, da Amadu Babba, Hadi Sirika. Yawwa to Kai da kanka sai ka auna , idan Amadu Babba ya samu minene makomar Dangiwa a siyasance, haka Kuma Idan Dangiwa ya samu minene makomar Amadu Babba a siyasance?

 

Yazid Nasudan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here