DAME KORAU ZAI NEMI KURI’AR MUTANEN KARAMAR HUKUMAR RIMI

0

DAME KORAU ZAI NEMI KURI’AR MUTANEN KARAMAR HUKUMAR RIMI

 

Budaddiyar wasika ga Danmajalissar Jiha mai wakiltar karamar hukumar Rimi a jihar Katsina.

 

Ranka ya dade na san ya zuwa yanzu hankalinka a kwance ya ke saboda ganiin cewa kaci zaben fitar da gwani a jam’iyyarka ta APC. Wannan ne ya sa ma ya zuwa yanzu baka cika daga waya ko maido sakon kar ta kwana ba ga wasu abokanan siyasarka, ko dai wadanda kuka yi takara tare ko kuma wadanda suka yi takara sama da kujerarka ba su samu nasara ba, domin kai a ganinka ka maimaita kawai.

 

Ba guri na ba ne kar ka maimaita, abin da nake son nisar da kai shi ne ka gyara kurakuranka domin ciyar da karamar hukumar Rimi gaba.

 

Koke na na farko zan fara ne da yankin da na fito wato Mazabar Fardami, ranka ya dade kafi kowa sanini matsalar da wannan mazaba take fama da ita, amma har zuwa yau din nan baka taba kai koke a majalissa ba domin ganin yiwuwar yin wannan gyara ko akasin haka. Da farko kafi kowa sanin yadda hanyar Tokawa-Bidi-Yarmudi zuwa bakin gada ta lalace amma ko sau daya baka taba tunanin kai wannan koke ba.

 

Haka kuma kasan yadda dam din Tokawa-Bidi-Yarmudi ya ke neman kafewa kuma ka san amfanin wannan dam din ga al’ummar da suka yini cikin rana suka zabe ka, amma baka kai koken a yasa wannan dam ba har zuwa yau din nan.

 

Ranka ya dade kasan halin da ilimin wannan yanki yake ciki musamman Firamare din Yakasai wadda take daukar manyan garuruwa biyu kuma tazararta da garuruwan ya kai kilomita daya, sannan Block daya ne da aka gina tun 1972 sai sabunta shi da ake, kasan yawan daliban da ke wannan makaranta, amma ka gaza kai koke a kara mana Block daya, wanda yasa dole ake hade yan aji biyu da daya a aji daya da kuma yan aji uku da hudu da biyar da shidda duk a aji daya, wanda hakan ya ke barazana ga ilimin yaran, amma da yake ba yaranka ba ne, diyan wadanda ka ke ci da guminsu ne sai ka banzatar da wannan koke wanda har tura ma shi na taba yi.

See also  ‘Yan sanda sun kama dan aikin gida, da ya kashe ogan sa

 

Bayan wannan akwai massalacin juma’a da aka fara a Yarmudi da ka je kamfe har maganar shi aka taba yi ma, amma shiru kake ji malam ya ci shurwa.

 

Korau ba ka da wani aikin daya na raya al’umma da zaka nuna kace kayi a wannan mazaba tamu, suma Exco din da suka sake zabarka baragurbi ne a mazabar kuma basu san kome ba face kansu, basu da tunanin makomar yaransu a gaba, kansu kawai suka sani.

 

Idan muka koma a kafutanin karamar hukumar Rimi, ko a cikin Kwaryar Birnin Rimi a kwai abubuwa da yawa da yakamata ace kamkai korafin yin su, misali sabunta hanyoyin cikin garin Rimi, Daukakawa tare da daga darajar Asibitin Rimi, da sauran abubuwa da za a dade ana tunawa da kai, amma sai ya kasance ba abin da kake sai dumama kujera a majalissa da kuma ci da guminmu.

 

A bangaren ilimi mu bamu san ma akwai ka ba, domin ko Dan tirenin din nan na Jamb ya kamata ka bude shagon da za a rika koyar da wadanda kake ci da guminsu.

 

Ya na da kyau ka sani Farfagandar da kasa wasu wadanda kai kanka kasan marasa kishin kansu ne da garinsu suke ma a social media ba za ta kaika ga hanya mai bullewa ba, domin mu yanzu zamu fito mu sanar da mutanen mu a nan da kuma a zahiri muhimmacin zaben wanda ke kishin sumda garuruwansu ba wai ci da guminsu ba.

 

Ba zai yiwu ba mu baka dama tsawon shekara hudu ka gaza tabuka mana kome, sannan ka yi amfani da karfin mulki da na kudi ka sayi Daliget ka kuma yi tunanin mu ba zamu sanar da mutanen mu muhimmancin zaben wanda zai amfane su ba, kar ka yi tunanin kana Jam’iyyar Buhari da Masari wannan daban mu ka fiye mana su, tunda kafi kusa damu.

 

Ina mai baka shawara da ka gyara halayenka ka rungumi mutanenka ka shiga cikinsu ka ji korafe-korafensu domin kai wa gaba, kuma ka jajirce ka tabbatar da an yi masu.

 

Mai maka fatan alheri

Abdurrahman Aliyu

A madadin masu kishin karamar hukumar Rimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here