DAN TAKARAR GWAMNA ZAI CIWO BASHI MAI TSADA
Daga Taskar labarai
Wani Dan takarar gwamna a Katsina a wata jam’iyya na tattaunawar yarjejeniya da wani attajiri daga wajen jihar Katsina don ya zuba jari na ba da kudin da za a ci zabe shi kuma a bashi ragama mai karfin gaske a tafiyar da mulkin da kuma biyanshi kudin shi da riba mai yawan gaske.
Wata majiya ta shaida mana cewa, an kiyasta lissafin abinda ake tsammanin za a kashe da abin da ake bukata a wajen sa.
Majiyarmu tace wannan dan jari hujjan ya amince zai zuba jarinsa a zaben na Katsina don ya samu karfin iko da ribar da yake jin zai samu.
Majiyarmu tace an daddale akan ribar da za a bashi an kuma daddale akan mukamai na gwamnati da za a bashi, don su sa Ido ga ayyukan da za a Rika bashi.
Wani abin takaici wanda ake tattaunawar da shi ya zuba jarinsa a zaben sam-sam baya da alaka da Katsina da mutanenta ta kowace hanya.
A lissafin su, Buhari zai fadi zabe, Don Haka Katsina za ta zama ta mai rabo, za a zo da abin arziki a watsa kamar yadda ake watsawa yan tsaki tsaba, daga nan Al’ummar Katsina sai su shiga wasoso, daga nan sai a lakumen zaben.
Majiyarmu tace an yi zama biyar akan lamarin a garuruwa daban-daban an kuma cimma manufa da matsaya. Ciniki ya Shiga sai bayar da awalaja, an yi cinikin makomar Katsina.
Za a shigo masu da kudin bashi a watsa, don suyi wasoso kamar Yan tsaki.
Taskar labarai zamu Kara zurfafa bincike, kuma mu fallasa komai daki daki dalla dalla.
_________________&_____________________________________
Kana son labarai na musamman? Bincike na musamman? Jeka turakar Taskar labarai dake www.taskarlabarai.com da sauran turakar sada zumunta na Taskar labarai.