FARFAGANDA BA TA CIN ZABE: BUDADDIYAR WASIKA GA KANTOMAN KARAMAR HUKUMAR RIMI

0

FARFAGANDA BA TA CIN ZABE: BUDADDIYAR WASIKA GA KANTOMAN KARAMAR HUKUMAR RIMI

 

Ranka ya dade ina fatan kana lafiya, kamar yadda na ke zato.

 

Duk da kasancewata Bakauyen da ya fito daga kauyen Yakasai a Mazabar Fardami da ke gundumar tsagero a Karamar hukuma mai albarka ta Rimi, kauyanci na da kuma farfagandar da ka sa ake maka ba zai hana rubuto maka wannan budadiyar wasikar ba, domin in nusar da kai da mutanen yankin Tokawa da Yakasai da Yar’mudi da Damusau wasu abubuwa da kila kuka manta ko kuma kuka sani kuka take sani, ganin cewa mutanen da ke yankin kauyawa ne marasa ilimin boko a tunaniku.

 

Da farko ni a matsayina na matashi da ya fiti daga yankin wadannan garuruwa guda hudu da kuka mayar sanuwar ware ina son in sanar da kai cewa su dai ne ke iya cin zaben wannan mazaba ta Fardami, kuma ita ce mazaba daya tilo da ta sha kafa tarihin zaben kansila a jam’iyyar adawa, duk saboda wariya da kuke nuna wa mutanen wadannan garuruwa, amma sai kusa ai ta yi maku farfaganda, to yana da kyau ku sani yanzu kan mage ya waye, kuma kunnuwan jakki basu ba kura tsoro.

 

Ina neman alfarmar Maigirma kantoma ya duba wasu bukatun wadannan garuruwa ya ga abin dazai iya yi, kafin mu sanya kafar wando daya da Jam’iyyar APC.

 

1. Matsalar ruwan sha na daya daga cikin abubuwan da suke ci wa wannan yanki tuwo a kwarya, Kantoma ka sanya yaran ka sun sanar cewa ka gyara fanfunan Bidi da Tokawa da Yar’mudi, tabas an gyara famfo daya a Bidi, amma a Tokawa ba a gyara ba an ce Kansila ya ba Ciyaman na Fati kudin gyaran, kamar yadda ka bayar, amma dai ba a yi gyaran ba, sai ka binciki ciyanman din Fati na mazabar ka ji in da batun ya kwana.

 

2. Tabbas na gyara makarantar Firamare ta Yakasai, mun gode, amma in da gizo ke sakar shi ne, tun kusan wata hudu da suka wuce Dan kwangilar ya tona ramukan yin Masai, amma har yanzu ba amo ba labari an bar ramukan da buloluwa an ki zowa a yi ginin ramukan sun zama barazana ga dalibai, sannan in malami zai zagaya sai ya yi tafiya sama da ta rabin kilo mita domin ya kauracewa in da yara za su iya hango shi. Ya mai girma kantoma wannan na san ko cikin aljihunka ka iya sanyawa a yi wadannan kewayoyi.

 

3. Mutanen wannan Yanki na bukatar cikon kasa ga gyara ramuka tsakanin hanyar da ta tashi daga Tokawa-Bidi-Yarmudi zuwa bakin Gadar Kanyar Uban Daba, ranka ya dade mun san wannan babban aiki ne, amma muna bukatar a yi mana ciko da gyare-gyare koda na tifa ashirin ne a bisa hanyar domin jin dadin zurga-zirga.

 

4. Mayar da Mutanen Tokawa da Bidi da Damusau da Yar’mudi Sanuwar ware. Wadannan garuruwan su ke da mafi rinjayen kuri’un da ake cin zaben mazabar da su, amma da aka tashi ba da mukamai na siyasa, sai aka mayar da wadannan garuruwa sanuwar ware, misali an bayar da Kansila a cikin Fardami, haka kuma an bayar da S.A a cikin Fardami, ka yi kwamitoci da yawa amma baka dauko ko mutum daya ba daga wadannan garuruwa ka sanya shi cikin wani kwamiti da zai bada gudumuwa a karamar hukuma.

 

Yana da kyau Mai girma Kantoma ka sani wadannan garuriwa akwai masu ilimi tun daga matakin firamare har digiri na biyu a cikinsu, kuma shirye suke su bayar da gudumuwa wajen bukasar Karamar hukumar Rimi, amma sai ka yi watsi da su. to muna tunatar da kai cewa ya kamata a diba wannan batu sosai.

 

5. Mutanen wannan yanki shirye-shiryensu ya yi nisa na gani sun samu Community Secondary school a Fardami domin rage zurga-zurga da kuma tabbatar da wanzuwar ilimin boko a garuruwan Tokawa da Bidi da Yarmudi da Damisau da Yartsamiya da Yargwamna da sauran garuruwan da makarantar sakandire ta ke da nisa a tsakaninsu, muna so mai girma Kantoma ka shiga cikin wannan tsari kuma ka taimakawa mutanen wannan yanki, su samu wannan makaranta.

 

Babu shakka mu mutanen kauyukan Tokawa da Yarmudimda Yakasai da Damisau muna biyayya ga Jam’iyyar APC da manufofinta, amma ko shakka babu zamu iya sauya musamman saboda sanuwar ware da aka maida mu.

 

A takarda ta ta gaba kuma zan yi magana ne kan Dam din Tokawa da Yakasai da Yarmudi tun daga tarihin kafuwarsa da kuma durkushewa da yake faman yi karkashin mulkin APC, sannan zan yi magana kan asibitoci da halin da suke ciki. Da kokarin Kantoma na ganin ya dauke Kasuwar Rimi zuwa lamba kamar yadda ake rade-radi.

 

Ina fatan Maigirma Kantoma zai kalli wannan takarda tawa da idon Basira, sannan ina fatan ba zai mata kallon siyasa ba.

 

Abdurrahaman Aliyu

A madadin matasa masu son ganin cigaban Mazabar Fardami, da Karamar hukumar Rimi baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here