LABARIN TARON SIRRI NA PDP DON FITAR DA JIGOGIN YAKIN NEMAN ZABE!

0

LABARIN TARON SIRRI NA PDP DON FITAR DA JIGOGIN YAKIN NEMAN ZABE!

Daga Taskar labarai

Wata majiya mai tushe ta fadawa Taskar labarai yadda PDP ta yi wani zaman sirri a wannan makon ta fitar da wadanda za su jagoranci kamfen na Yakubu Lado/ Majigiri a kakar zaben da za a shiga.

Majiyarmu tace da aka zo wajen zaman sai wasu daga cikin.
mahalarta suka ce a zabi Alhaji Ibrahim Dankaba ya zama DG na kamfen din, wasu kuma suka ce a zabi Lawal Rufai.

Sai Dankaba yace ya bar wa Lawal Rufai shi ma Lawal Rufai yace ya barwa Dankaba,ana cikin haka sai Majigiri da Lado su ka yi wani kus-kus, sai su ka ba da shawarar da Lawal Rufai da Dankaba su fita waje, koda suka fita sai Dakta Matazu yace Sam bai kamata a ba ko daya daga cikin su ba.

Saboda suna da kes a EFCC kuma ana tuhumarsu, ana zuwa kotu dasu, Dakta Matazu ya gamsar da taron, sai kuma Lado ya yafuto Majigiri suka sake kus-kus. Sai kawai akace aba Alhaji Sani Abu Minista, duk sai aka amince.

Sai aka ce su Dankaba da Rufai su dawo ciki suna dawowa aka fada masu matsayin da aka dauka suka ce sun amince yayi, za su yi aiki akan haka.

Daga nan sai aka zabi Alhaji Ibrahim Dankaba mataimakin DG Yankin Katsina, sai kuma Dakta Matazu mataimakin DG kamfen yankin Funtua shima kuma Lawal Rufai aka bashi shine sakataren kamfen din baki daya.

See also  SUNAYEN HAUSAWA DA MA'ANONINSU.

Da aka zo zaben mata, sai Hamisu Gambo Dan Lawan Katsina ya ba da shawarar a baiwa Bilkisu Kaikai shugabar mata, ya kawo hujjar da kowa ya amince.

Sai Lado ya dunguri kafar Majigiri, sai suka yi kus-kus sai aka ce ga tsarin kamfen na bangaren Mata.

Hadiza Muhammad Maikudi Kankara tsohuwar S.A Intergovernmental ita ce DG ta Mata yankin Funtua, Bilkusu Kaikai DG ta Mata Daura zone sai wata yarinya ‘yar gaban goshin Maryama Umaru Musa Yar’adua wadda ake kira da Jaringe ita kuma DG ta Mata Katsina zone.

Majiyarmu tace yadda akayi taron kamar dama an tsaro shi daga wani waje sai kawai aka zo nan aka tabbatar da shi, ta kara da cewa yadda aka ga Lado yake sarrafa Majigiri abin da burgewa.

Majiyarmu ta ce ana mamakin ya za ayi Sani Abu Minista ya jagoranci​ DG kamfen mutumin dake tafiya da sanda? Kullum cikin magani? Sai dai in ana son DG jeka nayi ka ne, ko akwai wata a kasa!
________________________________________________________
Labarai na musamman bincike na musamman jeka turakar www.taskarlabarai.com da shafukan Facebook da twiteer. da Youtube da Instagram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here