MUTANE GOMA DA SUKA FI KOWA AMFANI A GWAMNATIN MASARI

0

MUTANE GOMA DA SUKA FI KOWA AMFANI A GWAMNATIN MASARI

#JaridarTaskarLabarai

Daga Abdulrahman Aliyu

2. Hon. Salisu Hamza Rimaye

Shi ne Danmajalissa mai wakiltar karamar Hukumar Kankiya a jihar Katsina, ya fada cikin wannan kason ne saboda bincike da aka yi aka gano wasu abubuwa guda uku da yake da su wanda kaf din ‘yanmajalissun jihar Katsina babu wanda ke da su, kuma abubuwan suna zuwa ne kai tsaye ga talakka.

Abu na farko a kafatanin ‘yan majalissar dokokin jihar Katsina babu wani wanda ke da wata Gidauniya ta taimakon talakawa sai shi, wato gidauniyar Maigemu Foundation.

Wannan gidauniya ta kasance wata madogara wadda talakwan da ya ke wa wakilci suke rabewa su samu biyan bukata, a karkashin wannan gidauniya ta shi, marayun da ke Kankiya kaf din su basu kukan rashin abinci ko kayan Sallah, domin wannan Gidauniya tashi ta masu rijista kuma tana daukar nauyin dunkunan su duk salla, sannan kuma a karkashin gidauniyar akwai bangaren Lafiya wanda kebayar da magani da daukar nauyin aiki kyauta wanda bai fi karfinsa ba, sannan akwai bangaren ilimi in da yake bayar da Tallafi karatu ga wasu da kuma daukar nauyin wasu zuwa wasu makarantu.

Shi kadai ne Danmajalissar jihar da ya fara koyar da Ilimin kwamfuta ga al’ummar mazabar shi kuma har aka samu wadanda suka bude shaguna da kuma samun aiki duk ta dalilinsa.

Shi ne Dan Siyasa daya tilo a duk fadin jihar Katsina da ya jagoranci tara matasa yan jagaliyar siyasa sama da Dari biyu ya sa aka basu darasi kan illar bangar siyasa da kuma shaye-shaye, sannan ya yi masu alkawarin duk wanda ya shiryu zai bashi jari.

Wani babban dalilin da ya sa aka zabe shi daya daga cikin mutane goma masu amfani a gwamnatin Masari shi ne an tabbatar da cewa aikin shi don talaka ya ke yinsa, kuma bai gudun mutanensa, sannan wasu ‘yanmajalissa sun yi koyi da shi wajen bude gidauniya domin suma su tallafi jama’arsu, sannan wasunsu sun yi koyi da shi wajen koyar da al’ummarsu ilimin Kwamfuta.

Haka kuma gidaumiyar shi ta Maigemu Faumdation ba ta siyasa bace, kowa na amfana da ita PDP da APC.

Wannan dalilin ne ya sa baki daya zaben fitar da gwani da aka yi ba a samu wani danmajalissa da ya kama kafarsa wajen kuri’u ba, domin dudu abokanan takararsa ba su wuce kur’u hamsin ba.

A bangaren kyautatawa ‘yan siyasa an shede shi da cewa hannusa bude yake ga al’ummarsa, sannan kuma shi ne Danmajalissa daya tilo!da ya rika wo abinci yana kawowa a lokacin zabukan fitar da gwani da suka gabata.

Duk da irin wadannan tarin ayyukan alherin na sa Hon Salisu Hamza Rimaye shima bai cike goma cif ba, domin ana ganinsa mutum mai zafin magana, wanda bai barin ta kwana da ka yi masa zai mayarma, wanda kuma ya kamata ace dan siyasa ya guji haka.

Jardar Taskar Labarai na yi wa Hon Salisu Hamza Rimaye fatan alheri. Musamman kasancewarsa mafi amfani a ‘Yanmajalissar dokokin jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here