TABARGAZAR KANTOMOMI KANANAN HUKUMOMI A KATSINA
Daga Taskar labarai
Jaridar Taskar labarai ta yi wani bincike na musamman akan yadda kantomomin da aka nada suka rika aiwatar da tabargaza daban-daban suna shiga ofisoshinsu da kama aiki
Taskar labarai ta boye sunayensu da kananan hukumominsu.
Bisa wasu dalalai amma duk abin da zamu kawo muna da hujja kuma wanda yasan wanda ake magana a kansa ya sani.
In ta kama zamu fadi suna wasu ma har da wasu takardun ko hotunan da muke dasu za mu yi hakan.
Wani kantoma ana nada shi sai yaje ya ciwo ma karamar hukumarsa bashi na miliyoyin nairaa banki, don haka ana fara basu kudin farko daga jiha sai banki ya rike kudin ya ce an fara biyan bashi.
Wannan ya sanya ma’aikatar kananan hukumomi ta rabawa bankuna cewa kar kantoman da ya mara cin bashi ga karamar hukuma ba tare da amincewar ma’aikatar kananan hukumomin jiha ba.
Taskar labarai taga wasu takardun da suka shafi wannan kantoma da karamar hukumar sa. Wani kuma ana bashi kudin da zai yi aiki dasu sai kawai ya canza masu mazauni zuwa asusunsa na kashin kai. kuma yayi mirsisi sai da ta kai an buga masa waya ance kudin bana ubansa bane.
Kuma aka yi masa gargadi mai kauri, ai sa ya yi maza ya maida su a asusun karamar hukumar, mun ga takardun da aka rubuta na koke akan sa.
Wani kuma lulawa ya yi ya tafi birnin turawa yana bude ido da shakatawa bamu da wani tabbacin Koda kudin kananan hukumomi ya tafi amma tabbas yayi tafiyar kuma ya dau kwanaki a can.
Wani kuma kudin aiki aka tura !asa aka kuma tura masa dan kwangilar da zai yi aikin yace me uban kuturu yayi kadan shi zai kwangilar sa don ya samu abin sanya ma bakin salati Abinci.Yace shi ne gwamnan karamar hukumar sa har da takai cikin fushi a kace masa inji uban wa? Dai dai yake da gwamna? Gwamna zaben sa aka yi shi kuma nada shi aka yi.
Wani kuma kara’i ya/yi na jin dadi, da bai yi ba a baya, kullum yana otel kwance. binciken ya tabbatar mana yanzu haka otal uku na binsa bashin kudi sun kai rabin milyan baya neman !mata shi dai ya kwanta a AC yasa a kawo masa sakwara da ganda in kana neman sa yace samar ni daki na kaza, da ka iso ya danna waya yace me za a kawo maka?
Wani kuma gidansu na gado ya fara rushewa da canza masa fasali da yi masa kwalliya abin kallo a garin.
Daga cikin su akwai wanda aka kasa a aure ana gab da daure auren aka bashi kantoma ya lalata tsohuwar maganar ya biya wancan abinda ya kashe yanzu lokaci kawai ake jira a daura dashi.
Taskar labarai taga wani tela da yake fantamawa a wani gari a wata karamar hukuma aka ce telan kantoma ne da ‘yan majalisar sa an ce kudin farko da aka samu aka aiki telan yayi masu sayayyar yadi kala-kala ya kuma dauko hayar wasu teloli sukayi masa dinki kala daban daban don su ma su shigo gari, kowane kansila a karamar hukumar aka yi masa irin dinkin man na kafi girman jikinka.
Wasu ana zargin da an samu kudi rabawa suke kamar yadda ake kason kayan gado.
Taskar labarai tayi magana da wani DAF bisa amana yace kusan hakan ne, don kuwa kasa kudin uku ake yi ka shi daya ai aiki kashi daya a taimaki jama’a kashi daya kuma kantoma da ‘yan majalisar sa su tada komada daga baya a ciccike takardun yadda aka sarrafa kudin.
Jaridar na ciga da tattara bayanai akan kantomomin da yadda mukamin ya canza rayuwarsu da yadda suke mu’amala da sauran ‘yan kananan hukumomin su.
__________________________________________________________
Labarai na musamman, binciken musamman jeka shafin Taskar labarai www.taskarlabarai.com da shafin Facebook, twitter, da instigram da YouTube.