ZIYARAR​ MU GARIN DAN MARKE A JAHAR KATSINA.

0

ZIYARAR​ MU GARIN DAN MARKE A JAHAR KATSINA.
Daga Taskar labarai
Tawagar Taskar labarai ta Kai ziyara a Garin dan.marke a karamar hukumar kankara.garin da aka haifi Sanata yakubu lado Dan marke Dan takarar gwamna a jam iyyar PDP.
A kusa da gidansu yakubu lado mita kadan alluna zaka gani na jam iyyar APC da hoton Buhari da. Masari sai kuma TATa a gefen hoton .
Wasu matasa ke kula da hotunan dare da Rana .sunce wai kyauta suke aikin ba Wanda ya Sanya su suka sa kansu Don nuna godiyarsu ga wata rijiyar burtsatse da akAyi masu kyauta Bayan tsawon lokacin da suka dauka suna fama da matsalar​ ruwa.ba Wanda ya taimaka masu
Mafi yawan mutanen da muka zanta dasu a Garin sun ce .takarar yakubu lado Bata dame su ba..Don a baya ma da da yayi takara yaci me akayi masu ?
Sanata yakubu lado Yana da gida Amma iyalinshi sun dauk shekaru basa zaune a garin..Haka. Ma gidan da aka haife shi Yana nan Amma mahaifinshi baya zaune a garin .munje gidan babban wan mahaifinshi .. sarkin noma shima ya rasu sai wasu ke zaune a gidan.
A takaice abin da muka gani da ji . yakubu lado Yana bukatar komawa gida Don jawo hankalin mutanen sa gare shi .Don kuwa basa tare Dashi.
Kalli wasu daga cikin hotunan da muka dauko a Garin gaba kadan zamuyi sharhin musamman akan ziyarar da abin da muka gani muka kuma ji.
__________________________________________________________
Taskar labarai jarida ce mai rijista da aka kafa ta Don bada labarai . ingantattu.sahihai ..a Bisa yanar gizo .kwararru ma aikata ke gudanar da ita .tana Bisa shafin.www.taskarlabarai.com da sauran zaurukan . Facebook Twitter.instigaram da YouTube.

Wannan allon tsakaninsa da gidan da aka haifi yakubu lado ..mita ashirin da bakwai ne

Gidan da aka haifi yakubu lado ..wani mai gadi ke kula dashi..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here