PDP A KATSINA ZA TA CHANZA TSARIN YAKIN NEMAN ZABEN TA

0

PDP A KATSINA ZA TA CHANZA TSARIN YAKIN NEMAN ZABEN TA

Daga Taskar labarai

Taskar labarai ta jiyo daga majiya mai tushe cewa jam’iyyar PDP zata canza tsarin wadanda za su jagoranci yi mata yakin neman zabe a jihar. Ba kamar yadda aka amince ba a wani taro da jam’iyyar tayi a Katsina.

A taron na Katsina, kamar yadda wannan jaridar ta kawo labarinsa an fitar da sunayen wasu da sune zasu tallata dan takarar su har ga nasara a PDP.

Dan takarar Sanata Yakubu Lado ya kira wani taro a gidansa dake Kano ( kun San Kano yake zaune,iyalinsa, wasu daga cikin ‘yan uwansa da mahaifansa tsawon shekaru sai takara-takara yake zuwa Katsina.

A wajen taron da ya yi da wasu amintattunsa sun canza fasalin wadansu da za su jagoranci yakin neman zaben, wasu kamar yadda zaman Katsina ya tsara, za a barsu, wasu kuma za a canza masu matsayi, wasu za a cire su kwata-kwata.

(Mun samu cikakken yadda tsarin yake amma muna kokarin tabbatarwa kafin mu bayyana shi)

A taron an zargi inijiya Muttaqa Rabe Darma da cewa shi ne ya baiwaTaskar labarai, labarin taron Katsina wanda taka kawo shi daki daki dalla dalla kamar Fim.

Kuma akwai yiyuwar kwamitin yakin neman zaben Lado zai sakawa injiniya Muttaqa Rabe Darma takunkumin bai kara gayyatarsa taronshi, ba zai san me ake ciki ba, ya ake ciki sai dai yaji da ganin ana yi.

In kuma an kafa gwamnati sai dai yayi gudun hijra( kurunkusa) inji wata majiyar da ta shaida mana.

Taron na Kano ya yi tsare-tsare da canji ga matsayar zaman Katsina wanda za a sake haduwa a nan Katsina a tabbatar da jaddada matsayin da aka dauka a taron Kano.

Takarar ta dan takara PDP na fama da talauci, ( ya zuwa yanzu) kamar yadda binciken mu ya tabbatar dan takarar gwamna bai fara fito da kudinsa ba, kuma ba abin da ya fara shigowa na aiki sai dai kowane dan jam’iyya na amfani da kudin aljifunsa a matsayin sadaukarwa.
____________________________________ **___________________
Taskar labarai jarida ce dake da cikakkiyar rijista a matsayin Jarida da ke bisa yana gizo tana bisa shafin www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta na Facebook, Twitter, instigram, da Youtube.
Tana bada labarai na musamman da bincike na musamman da hotuna da bidiyo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here