‘YAN PDP KU YI SHIRIN KO-TA-KWANA
-Yakubu Lado Dan Marke
*Daga Taskar labarai*
Dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a jam’iyyar PDP, Alhaji Yakubu Lado Dan Marke, ya fada wa magoya bayansa cewa; su yi shirin ko-ta-kwana, duk wanda ya takale su, su mai da masa martani.
“Duk wanda ya lakaci hancinku, ku mai da masa. Kar ku ce za ku bugo mana waya, don ba abin da za mu yi maku,” inji shi.
Ya ce; “Nijeriya kasar kowa ce, kuma ku ma ‘yan Nijeriya ne. Don haka kar ku takali kowa. Ku zama masu bin doka da oda, amma in an taba ku, ku rama.”
Alhaji Yakubu Lado Dan Marke, wanda ke jawabi a taron kaddamar da Kwamitin yakin neman zabe na jam’iyyar PDP da aka yi yau Juma’a a Sakatariyarta da ke Katsina, ya jaddada cewa; “Kar wani jami’in tsaro ya ce zai bude maku idanu. Ku jajirce, ku tsaya kyam. Sai an cire tsoro da rashin kwadayi za a kai ga nasara.”
Ya nanata cewa in aka zunguri hancinku kuka kawo mana koke, ba za mu saurare ku ba. Ku rama in an taba ku.”
Ya hakikance cewa; “Za mu tafi zabe a jam’iyyar adawa, wadda ba kudin gwamnati ce a hannunta ba, don haka kar wani ya yi tsammanin za a samu kudi. Abin da ya kamata ku yi shi ne in an ba ku kudin zabe, ku kara da naku. Samun amfanin abin sai an yi nasara.
“Kar kuma a rika damun ‘yan takara da bukatun ‘ai mana kaza, ai mana kaza.’ Ba kudi, tunda Baitul Mali ba hannunmu take ba.”
Ya kuma kara da cewa; “Kwato Jihar Katsina da kasar ke a gabanmu. Jiharmu ta lalace, duk wani gogaggen Dan Daudu, da wata kwararriyar Karuwa ta san da zaman Jihar Katsina, kuma ta mai da ita mafakarta.”
Ya koka da yadda ake karkatar da kudaden Jihar Katsina; “An ce ba kudin da za a yi mana aiki a Jiha, amma ana da kudin da za a bai wa ‘yan shagali masu bata wa yaranmu tarbiyya.
“Ana ta sace kudin Jihar ana kai wa kasashen waje da kuma sayen kaddarori a wasu jihohin. Ana gasar gina gidaje na kawa, isa da alfahari. Duk abin da ke faruwa mun sani, kuma shi muke son mu gyara,” inji Alhaji Yakubu Lado.
Ya ce; “In mun zo ba satar kudinku za mu yi ba, aiki za mu yi maku. Kowa ya san Yakubu Lado dan kasuwa ne. Ya san Atiku Abubakar dan kasuwa ne.”
A wajen taron an shelanta Alhaji Sani Abu Minista a matsayin DG kamfen, sai Dakta Shehu Garba Matazu a mataimakinsa a shiyyar Funtua, Alhaji Namadi Dankama; mataimakinsa a shiyyar Katsina, Maigemu Bindawa; mataimakinsa a shiyyar Daura, Hajiya Bilkisu Kai-Kai, DG kamfen ta mata; sai Lawal Rufai, Sakataren tsare-tsare kamfen din.
Yakubu ya ce nan gaba za a yi wasu kwamitocin daban har da na rumfa-rumfa.
__________________________________________________________Taskar Lbarai, jarida mai cikakkiyar rijista da ke Yanar Gizo na www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta na Facebook, Twitter, Instigram da You Tube.
Ziyarce mu don hotuna da labarai na musamman.
………….