BARAKA A TSAKANIN LADO DA MAJIGIRI

0

BARAKA A TSAKANIN LADO DA MAJIGIRI?

Daga Taskar Labarai

Wani rahoto mai inganci yazo mana cewa an fara samun baraka tsakanin dan takarar gwamna da mataimakinsa na jam’iyyar PDP.

An ce barakar ta kunno kai ne akan wa za a baiwa shugaban kamfen ta mata, an ce Yakubu Lado na son a baiwa Hajiya Bilkisu Kaikai a matsayin ita ce shugabar matan kamfen din baki daya, shi kuma Majigiri na ganin kamata ya yi a raba masu su uku, kuma kowa a bata cin gashin kanta, Duntua da Katsina da Daura.

Akan wannan ake ta samun matsala har zuwa yau da aka kaddamar da ‘yan kwamitin zaben, Wanda aka gabatar da kowa tare da tashi a gansa amma banda shugabannin Mata na kamfen din.

A wajen anga Jadiza Kankara da Bilkisu Kaikai sun cakara Ado sai dai ko kujera a bisa babban teburi basu samu ba. Wannan ya sanya suka fita waje suka samu wani ofis suka rakube.

Kuma wata takarda da jaridar nan ta samu ga sunan maza da matsayar su babu sunan mace ko daya, (duba takardar hade da wannan labarin)

Mun kira Jajia Bilki Kaikai don kin ta bakinta wayar ta bata shiga mun mata sakon waya ba amsa.

Taskar labarai ta kira shugaban jam’iyyar PDP kuma dan takarar mataimakin gwamna don Jin ta nakin shi, shima yaki daukar waya.

Sakataren tsare-tsare na jam’iyya shima yaki daukar waya daga baya yayi mana sakon cewa yana cikin mitin.

Idan wannan barakar ta tabbata ita ce sabanin farko da ya fara fitowa a tsakanin dan takarar da mataimakinsa.
__________________________________________________________
Taskar labarai na bisa shafin www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada zumunta na Facebook,Twitter, Instigram da Youtube.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here