AN KARRAMA SHAIHUNNAN MALAMAI TARE DA DANJUMA KATSINA.

0
493

 

AN KARRAMA SHAIHUNNAN MALAMAI TARE DA DANJUMA KATSINA.

Daga Taskar Labarai

Kungiyar marubuta ta kasa reshen jihar Kano (ANA) ta karrama wasu shaihunnan malaman Jami’a da suka yiwa harkar rubuce-rubuce hidima tsawon shekaru.

Taron karramawar na cikin taron da kungiyar ta saba yi duk shekara mai sunan satin marubuta, wanda akan dauki sati guda cur ana gudanar da jawabai da mukaloli akan yadda za a bunkasa harkar rubutu a kasar nan.

Taron na bana mai martaba sarkin Kano Muhammadu​ Sanusi II ya bude taro da kansa a Ranar 6/12/2018.

A Ranar lahadi 9/12/2018 aka rufe taron da bada kyaututtuka daga cikin wadanda aka baiwa kyauta akwai wasu makarantun boko da su ka yi nasara ga wata gasa da kungiyar ta marubuta tayi a tsakanin makarantun jiha akan adabi.

Sai kuma wasu fitattun mutane da kungiyar tace suna yiwa harkar rubutu, hidima a kasar na tace mutanen tsaye suka wajen ganin adabi ya bunkasa, suma wadanda aka baiwa adabin an kasa su kashi biyu.

kashin farko su ne Farfesa Abdallah Uba Adamu da Farfesa Mustafa Ahmad Isa da Farfesa Adamu Idris Tanko da Farfesa Aliyu Kamal da Dakta Bukar Usman da Dakta Bala Muhammad da Dakta Ismaila Bala da Injiya Y.Z Ya’u da Zaharadeen Ibrahim Kalla da Alhaji Badamasi Burki sai Muhammadu​ Danjuma Katsina.

Danjuma Katsina shi ne mawallafin jaridar Taskar Labarai dake bisa yanar gizo, wadda kan kawo rahotannin musamman, akan Al’amurran yau da Kullum.

Daga cikin marubutan da ka karrama akwai wadanda Allah yayi masu rasuwa, amma sun yi ma adabi hidima kafin rasuwarsu.
Su ne marigayi Hadi Alkalanci da malam Balarabe Sango da malam Balarabe Sari da Rukayya Maikafi da Abdullahi Mukhtar Yaron Malam.

Akwai Kashi na biyu da aka karrama sun hada da:
Malama Maryam Ali Ali da Aminu Ladan Alan waka da Maimuna Beli (wadda taci Gasar adabi na BBC a Bara) da Danladi Haruna.

An yi taron a dakin taro na babban dakin karatu na jihar Kano Mai suna Murtala Muhammed kuma ya samu halartar baki daga ciki da wajen Kano.

Daga Katsina akwai Alhaji Dikko Bala Kofar Sauri da Lawal Danja da Alhaji Sallau Arawa Co-ordinator na Hajiya Mariya Bala Usman da DG NPA sun yi wa Danjuma Kara sun hallarta.

Hon Mansur Ali Mashi (Dan majalisar Mashi/Dutsi) ya dau nauyin ‘Yan kungiyar Writer’s Bureu, Katsina chapter wadanda suma sun halarta don yiwa Danjuma Kara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here