JIGA-JIGAN PDP SUN YI TARON SIRRI A ABUJA

0

JIGA-JIGAN PDP SUN YI TARON SIRRI A ABUJA
Yakubu Lado yace baida programme ko blueprint

Daga Taskar labarai

A satin da muke a ciki ne wasu jiga-jigan jam’iyar PDP suka yi wani taron sirri a Abuja a ofis din tsohon gwamnan Katsina Barista Ibrahim Shema.

Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa taron ya hada da wadansu masu fada aji na jihar Katsina wadanda ke marawa jam’iyyar PDP baya da wadanda basa jin dadin yadda ake tafiyar da mulkin Katsina karkashin APC.

Taron ya samu halartar hatta dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Danmarke.

A taron wani jigo a PDP ya bayyana fushinsa da bacin ransa cewa an cuce su an kuma yaudare su, aka sanya suka zura jiki ashe suna da wata manufa boyayya ta dan takarar da aka tsara za a fitar, an ce a ka yi ta bashi /hakuri, aka ce yanzu abinda ya kamata a tattauna shi ne ya za aci zabe.

Wani daga cikin ‘yan taron ya kalli dan takarar Sanata Yakubu Lado yace wane tsari ( programme) ka ke da shi na ciyar da Katsina gaba?

Sanatan ya kalle su yace yanzu babu a tsarin a rubuce, amma suna iya tsara masa, ai nan wasu a cikin taron suka fusata? Wani Yace, what? Kana neman mulkin gwamna baka da wani tsari daka shiryawa jahar?

Nan Sanata Yakubu lado ya fara bayani saura suna s kalubalantar sa cikin fushi. An kuma tambayi Dan takarar wane ? kundi mulki har zuwa nasarar karshen mulkin ka kake dashi? Kundin da ya shafi gina jihar,tafiyar da mulkin jihar da dora ta bisa wani turba ingantacce?.( blueprint)

Sanata yace babu, amma a taimaka masa a tsara a tare nan ma suka fusata su ka ce kaje ka tsaro ka kawo sai mu inganta maka.

See also  MNDA COMMITTED TO PARTNERING WITH UK PACT, FCDO TO CHANGE LIVES IN N’DELTA REGION – SHARON IKEAZOR

Sun kuma tambaye shi ya zai dauki nauyin kamfen din sa ina za a samo kudi ? ( Funding)

Nan ne yace ana ta tattarawa da nema. Amma bai fadi a ina ake nema da tattarawa ba ya kuma ce za a samu abin da za a samu wajensa in aka hada za a samu abin yakin neman zabe sosai.

Dattawan wadanda mutanen kirki ne masu kishin jihar Katsina sosai sun fada masa cewa a matsayin su ba abin da suke nema a jihar sai cigaban ta kudi Allah ya basu har zuriyar su, mukamai sun rike daban daban yanzu sun kai sai dai su bada shawara.

Sukace masa ko gwamnatin PDP ta kafa huddarsu da ita sai dai a tarayya amma ba a jaha ba .
Fatansu daya ce jihar ta bunkasa da ci gaba tafi kowace jiha a kasar nan.

Ya roki dattawan da a taimaka masa a ci zaben in gwamnatin tazo a hannu duk wani maganar gyara tafiyar da mulkin da tsari mai kyau sai a tsara.
Wani a taron yayi korafin cewa , yakubu lado ya cika Katsina da fastocin takarar SA.amma Sam baya yin komai na tallata Dan takarar shugaban kasa Atiku anan ne yace ..ai Suma fastocin na Atiku ana can ya Sanya a buga..yace a baya sun yi kokarin. Sawa gwamnatin jaha ta Hana ..

Jaridar Nan tayi magana da wasu da akayi zaman dasu .kafin fitar da labarin..uku daga cikin su since zaman magana ce ta cikin gida..wadda Bata bukatar talla.daya kuma ya tabbatar da duk abin da jaridar taji daga wata majiya Mai tushe.
__________________________________________________________
Taskar labarai jarida ce dake da cikakkiyar rijista Kuma tana bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma shafukan sada zumunta na Facebook, Twitter, Instigram, da Youtube

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here