YUNKURIN KAWAR DA MASARI DA LADO YADDA SHIRIN YA WARGAJE

0

YUNKURIN KAWAR DA MASARI DA LADO
_____________YADDA SHIRIN YA WARGAJE !!

Daga Taskar labarai

Wani labari da muka samu daga wata majiya !ai tushe shi ne wani yunkuri da wasu da suka kira kansu masu kishin jihar Katsina su ka yi na samar da wani dan takara wanda zai amshi jihar Katsina daga APC karkashin Aminu Bello Masari
Majiyarmu tace mun hadu a Katsina da Kaduna da Abuja ama daban-daban Inda mukayi nazarin halin da jihar Katsina ke ciki karkashin APC Inda muka baje abin da muke da shi daga majiyoyi da suke tabbatattu ne, da wasu takardun da suka shigo hannunmu muka tattauna in Katsina ta cigaba a haka nan da shekaru hudi to abin Allah ya sawwaka.

Majiyarmu tace sai kuma muka ga mafi munin shi ne jam’iyyar PDP ta tsaida dan takarar da bai cancanta ba. Gaskiyar magana ma gara Aminu Masari da shi.

Mai ba jaridar nan labari yace mun hada duk ‘yan takarar a bisa fai-fai muka ga muna cikin halin gaba kura baya siyaki, don haka sai muka tsaida shawarar cewa a fitar da dan takara mai kyau ya fito daga wata jam’iyyar da take da dan takara,sai kawai canjin dan takara jam’iyya za ta yi,
Muka yanke amince da haka muka tsaya akan jam’iyyar PRP.

Har ma wani yayi magana da shugabannin PRP na kasa suka amince zasu marawa duk matsayar da aka yi baya, mai bamu labari yace, sai muka tsara yadda za a fara tuntubar mutane da kuma yadda za a tara kudi da yadda za ayi kamfen na ceto Katsina daga Masari ko Lado.

Matsalar farko da aka fara samu ita ce wani daga cikin taron ana zargin yaje ya kwashe ya fada wa Yakubu Lado duk abin da ake ciki.

See also  AN JINJINA MA JARIDUN TASKAR LABARAI

Matsala ta biyu sai muka je wajen Shema don neman goyon Bayan shirin, sai Shema ya gayyato Lado wajen zaman Abuja ya kuma ce mafita kawai a marawa Lado baya.

Wata majiya a APC akida sun tabbatar wa jaridar nan cewa da wancan Shirin ya dore da sun marawa duk wanda aka tsaida baya a kuma kowace jam’iyya ce banda PDP. kuma sun san da shirin sun kuma yi fatan yayi nasara, yace da APC Akida sun zauna da su anyi yarjejeniya sun kuma mara masu baya da komai nasu.

Mun samu magana da wani dake da alaqa da fadar shugaban kasa wanda yace da shirin ya yi nasara kuma suka gamsu da dan takarar da aka tsaida da za su tabbatar sun kyale zaben gwamna a Katsina ya tafi mai rabo ka dauka, zamu tabbatar zaben bai samu wani tagomashin karamci daga fadar shugaban kasa ba.

Yace suna bin shirin kuma sun shirya marawa duk dan takara baya in ba daga PDP yake ba.

Majiyarmu tace Shirin ana iya cewa ya mutu ko kuma ya suma idan suma ya yi ta ina za a tada shi? Ya bayyana kafin ya girma? Kan masu shirin ya rarrabu? Amma ba asan abin da gobe zata yi ba, inji majiyarmu.

_________________________
Taskar labarai jarida ce dake da cikakkiyar rijista dake bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter da Instigram da Youtube.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here