JAM’IYYAR APC A KATSINA NA TSAKA MAI WUYA INJI WASU MASU RUWA DA TSAKI

0

JAM’IYYAR APC A KATSINA NA TSAKA MAI WUYA
_________INJI WASU MASU RUWA DA TSAKI

Daga Taskar labarai

Wasu dattawa a jam’iyyar APC karkashin wata kungiya mai suna Concerned APC Members Forum sun gabatar da wani taron manema labarai in da a ciki suke cewa jam’iyyar na cikin tsaka mai wuya a Katsina.

Takardar wadda Alhaji Aliyu Sani Muhammed da Ambasada Yakubu Suleman suka sanya wa hannu sun yi kira da jam’iyyar ta/yi taka tsantsan a jahar.

Inda suka ce rarrabuwar kan dake tsakanin ‘yan jam’iyyar ta yadda har wasu ‘yan takara suka kai kotu wannan ba zai ma jam’iyyar da mai Ido ba.

Sun kara da cewa daga yadda wata kotun koli ta yanke wani hukunci a jahar Ribas, wanda matsalar iri daya ce da ta jahar Katsina, wanda idan aka cigaba hakan to jahar zata shiga gaba kura baya siyaki.

Alhaji Ali Sani ya yi zargin cewa wasu na tare da gwamnan basa fada masa gaskiya kuma basa son wasu su rabe shi saboda suna Jin cewa idan aka matso kusa da gwamnan za a rage masu fada.

Ali Sani ya bada misalin cewa an yi taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar amma babu wanda ya gayyace shi yace gwamnan ya taba cewa duk abin da za a yi a fada mani amma ba a gayyace ni ba.

Yace irin wannan sakacin da rashin jawo kowa a jiki na daga abin da ya jefa jam’iyyar a yanzu wasu ‘yan takara ke a kotu, wanda kuma irin matsalar Katsina irin tace kotun koli ta yanke hukuncin kwanan nan in da tace jahar Ribas a yanzu nata da ‘yan takara ko daya a APC.

Ali Sani da Yakubu Suleman suka ce in haka ta ci gaba APC na iya rasa dan takara a Katsina don haka, har shugaban kasa ma zai rasa jihar.

Ali Sani yace lokaci da shugaban kasa da na jam’iyya za su sanya baki don ayi wa lamarin tufka a tsaida shi haka nan.
Ya kamata duk wani dattijo ya shigo maganar a Katsina kafin ta ida lalacewa inji shi, domin in kotu tayi hukunci akan shara’ar bata da gyara, sai cabewa, don ba a san Inda jahar sa a gaba ba inji Ali Sani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here