TSAFI GASKIYAR MAI SHI: TASHAR BBC TA HADU DA WANI MAI IYA RUWAN SAMA
Daga Taskar labarai
Hausawa na cewa tsafi gaskiyar mai shi kuma Allah ya fadi a cikin Alqur’ani Mai tsarki cewa,
“Yana fitar da bawa daga duhu zuwa ga haske, amma wanda ya bace yana kara fitar da shi daga haske zuwa ga duhu”
Gidan talabijin na BBC Afrika sashen Turancin buroka wadanda ke bisa yana gizo sun gana da wani mutum mai suna Godwin a jahar Anambara wanda yace yana iya sanya ruwan sama ya sauko.
Mutumin Wanda yake boka ne irin bokan nan na kasar Inyamurai yace a kawo masa goro da irin giyar nan ta wuski ‘yan BBC su zo da kayan aiki a gabansu zai yi siddabarun da ruwan sama zai sauka.
Wakilan na BBc sun kawo ma bokan mai suna Godwin Onasade abin da ya bukata, inda nan take ya ja su zuwa wajen bautarsa. Yayi wasu kulumboto da wasu tsatsube tsatsube. Sai ga hadari ya hadu, sai ga ruwa yana sauka.
BBC sun ce duk karkarar an yarda boka Godwin yana iya sa ruwa ya na kuma iya sauka.
Wakilan BBC suka ce gaban su yana gama surkullensa sai ga ruwa, suka ce masana sun ce ba mai iko da yanayin amma a karon farko sun ga boka Godwin.
Wanda ke son yaba cikakken bidiyon ya je shafin jaridar Taskar labarai na Facebook ta dora shi daga BBC
Boka Godwin..Mai Sanya ruwa sama ya sauka
Hadari ya hadu.bayan ya Gama surkullensa
Boka Godwin Yana kallon sama Yana Kiran ruwa
Ruwa na sauka
__________________________________________________________
Don labarai na musamman shiga shafin Facebook na jaridar Taskar labarai da kuma turakarta dake, www.taskarlabarai.com da ko a shafukan Instigram da YouTube