KO INJINIYA KABIR BARKIYA ZAI CHANZA HALI IN YA ZAMA SANATA?
Daga Taskar labarai
wani bincike da jaridar Taskar labarai ta yi a kan rayuwa da aiki da injiniya Kabir Barkiya, wanda yake neman kujerar sanata a Katsina ta tsakiya karkashin jam’iyyar APC ya nuna shi ba mutum ba ne wanda ya dace da rayuwa ta siyasa.
Barkiya wanda yayi aiki har ya kai babban matsayi a gwamnatin tarayya har ya rike hukumar FERMA, daya daga cikin hukumomin masu tasiri a gwamnatin tarayya kuma a lokacin ya taka rawar azo a gani a mukaman da ya rike.
Bayanan sa na in da yayi aiki suna da kyau sosai , domin an shaide shi da aiki tukuru da yin mai inganci da tsare ka’ida da kamanta gaskiya .
Yayi aiki cikin mutumci ya kammala a mutunce. Ana kuma tuna shi ayyukan alheri da ya bari a inda yayi ayyukansa.
Amma rayuwarsa da sauran inda ya fito fa? tawaga mai karfi daga Taskar labarai ta yi tattaki har zuwa karamar hukumarsu ta kurfi da a garinsu na haihuwa Barkiya, abin da ta gano shi ne sam baya tare da mutanen karamar hukumarsa.
A garin Barkiya sun ce baya zuwa garin daga lokacin zabe sai wani lokacin na zabe ba su san shi ba, sai dai fosta in ance zai yi takara.
Fastarsa ta farko da ya nemi jam’iyyar PDP ta tsaida shi takarar gwamna da kuma yanzu da aka ce zai tsaya takarar Sanata a APC.
Mun zanta da shugabanin matasan Barkiya zantawa da aka yi cikin raha har da daukar hotuna na bidiyo da kuma hoto maras motsi. Sun fadawa ‘yan jaridar mu cewa duk cikar Barkiya da batsewarta, bai taba samar wa wani aiki ba koda kuwa na shara ne.
suka ce duk aikin da yayi a Abuja da mukaman da ya rike da damar da ya samu ba wani dan Barkiya da ya amfana da wannan damar, matasanmu sun gama karatu suna son su wuce ba taimako, wasu sun gama suna son aiki ba aikin,
hatta irin kuratan soja, dan sanda ko sauran masu kaki, babu a duk fadin Barkiya. Don kauye ce sai da wanda zai tsaya masu. Wanda Allah yayi wa daukakan ya tsaya bai damu ba.
Munje asibitin garin, wanda muka gani tana cikin hali tana bukatar taimako, shima ba wanda zai taimaka, wata kungiyar kasa da kasa na aiki amma aikin nata ragagge ne, ma’aikatan wadanda wasunsu yan asalin yankin ne, suna aiki da kishi da yin dubarunsu na yadda za su iya gudanar da asibitin da kan kansu, don in sun bari ta rushe sune suka rasa.
Ko Barkiya ya taba taimaka masu? Sam-sam koda kuwa da kwaran kafinol ne guda daya.
mun samu labarin wutar garin ta taba lalacewa, sai dai akwatin taimako suka daga.
“Nawa Injiniya Kabir Barkiya ya bayar?” ko kwabo inji wadanda suka nemi tallafin har aka gyara.
Mun je wani gidan kasa kusa da gidan maigari, an tabbatar mana shi ne kadai gidan da Injiniya Kabir Barkiya yake da shi duk barkiya, gida ne na kasa da mahaifinsa ya gina masa lokacin da za ai masa aure, nan yayi zaman angwanci da amarci da amaryarsa ta Ladar noma. Gidan yana nan yadda yake sama da shekaru talatin da suka wuce.
Wani dan Barkiya yace “kana ganin zaku iya tsammanin wani abun kirki daga wanda ya yi watsi da mahaifarsa? ya manta da mutanensa? ya juyama asalinsa baya?”
Kaje ka yi nazari inji wani dattijo a garin Barkiya, wasu a garin sun shaidawa tawagar jaridar cewa, sun ji wai yana da kirki amma inuwar giginyace na nesa ka shata, sai kuma ‘yan uwansa na kusa.
Mutanen garin Barkiya al’umma ce mai kokari, manoma kuma ‘yan kasuwa, an tabbatar mani suna da hazaka a wajen neman karatu. kuma suna zarra a duk abin da suka sanya a gaba, musamman in sun samu mai tallafa masu, fitattun mutane sun fito daga mazabar daga cikinsu har da dan majalisa mai wakiltar Dutsinma da Kurfi, Alhaji Danlami Kurfi da shaharraren dan jaridar nan edita a kamfanin Primium Times mai suna Ashafa Murnai Barkiya.
Barkiya gari ne mai muhimmaci, wanda ‘yan siyasa da ‘yan garin suka banzatar da muhimmancinsa a nan ne aka haifi Injiniya Kabir Barkiya dan takarar Sanata a Katsina ta tsakiya a karkashin jam iyyar APC.
Ko zai canza halinsa in ya samu nasara?
__________________________________________________________
Taskar labarai jarida ce dake da cikakkiyar rijista dake bisa anar gizo www.taskarlabarai.com da kuma kafofin sada zumunta na Facebook da Twitter da Instigram da Youtube da Whatsapp a lamba 07043777779