Kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya ta samar da hanyar koyawa matasa aiki

0

Kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya ta samar da hanyar koyawa matasa aiki

Daga Zubairu T M Lawal Lafia
A taron da kungiyar Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar a watan da ya gabata . Taron ya hada da wasu jungiyoyi na Duniya kungiyar Kwadago ta Duniya da Ma’aikatan matasa da wasanni ta qasa da kuma masu fada aji daga kungiyoyin alumma.

Taron dai ya gudanane a birnin Tarayya Abuja yadda ya maida hankali kan yadda matasa ki gudanar da rayuwar zaman kashe wanda ba tare da aikinyi na fari ko baki ba , a nan gida Nijeriya.

Dayake jawabi ga mahalarta taron Sakataren dindindin a Ma’aikatan Wasanni da Matasa Mista Adesola Olusade yace; yanzu haka muna fuskantar kalubale yadda qasarmu take da tarin matasa masu yawan gaske amma dayawansu basu da aikinyi.

Yace; da dama an sake qananan sana’o’in wadanda aka bada daga Iyaye da kakanni. Kowa yana bukatar ayyukan jin dadi .saboda wajibin mune mu samar masu da wasu hanyoyi na Sana’a wanda zasu dogara dashi su riqayi saboda yadda zasu gudanar da rayuwarsu.

Tunda farko Sakataren na dindindin saida yayi godiya masamman ga wadanda suka shirya wanan taron da kuma wadanda suka samu halarta taron.

Shima Mista Zulu Daraktane a Kungiyar Kwadago ta Duniya dake kula da wasu yankuna a nan Afirika kamar Nijeriya Ghana Liberia da Sierra-Leone. Yace; wanda ofishinsa
Yace; bubkasa harkokin Matasa ya zama wajibi a garemu saboda idan akayi la’akari da yanayin zamantakewan rashin aikinyi babban hatsarine a garemu samar da aikinyi garesu zaman Lafiyarmu ne ,dama nahiyarmu baki daya.

See also  Bayan daura Aure an kawoma ita gidan ka da safe taje alwala kaga fuskar ta koma haka ya zakayi?

Mista Zulu yace idan akayi la’akari da yawan matasa dake Nijeriya suna bukatar ayyukan yi da zasu gudanar da rayuwarsu na yau da kullun .

Shima Mista Sukti Dasgupta Babban Ma’aikaci a Ofishin kungiyar Kwadago ta Duniya yace; samar da Ilumin ayyukan yi kamar aikin kaki da harkan kasuwanci da Sana’a zaman kamar sabbin fasaha ire-iren kerekeren zamani abubuwane da ya kamata Gwamnotochi su mai da hankali wajen bunqasa shi a Jihohin su saboda matasa su samu aikinyi. Masamman tundaga Makarantun Kwalaji.

Ya kara da cewa Kungiyar Kwadago tana bukatar bada gudumawa wajen kirkirar ayyukan yi wanda zai taimakawa dubban matasanmu dake rayuwa babu aikinyi.

Tattaunawar da ya hada kungiyoyi da masu fada aji da vangaren Gwamnati ya tsaida matsaya yadda za’a samu a fidda rayuwar matasa daga kunci da zaman kashe wando.
Yace; kafin shekarar 2030 zamucimma wanan kudurin na rage yawan iftila’o’in da muke tattare dasu na matsalar matasanmu da kashi 15 .

Shima Ministan Kwadago ta qasa Sanata Chris Ngige yace; ma’aikatansa tana ta kokarin pfarfado da makamancin wanan kudurin da zai samar da ayyukan yi ga yan qasa.
Yace; yawan matasan da muke dasu basu amfanar qasar da komai shiyasanya tattalin arziki qasarmu yake ja baya a ko da yaushe . saboda duk qasar da take da tarin matasa kuma basu da ayyukan yi to qasar bata tasum cigaba a tattalin arziki.
Amma samun aikinyinsu shine cigaban tattalin arziki qasa .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here