Ma’aikatan Shari’a sun kara jaddada batun yajin aiki a Nasarawa

0
568

Ma’aikatan Shari’a sun kara jaddada batun yajin aiki a Nasarawa

Daga Zubairu T M Lawal Lafia

Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta jihar Nasarawa sun kara tabbatar da yajin aikin da ma’aikatanta keyi a fadin jihar. Shugaban kungiyar JUSUN ta qasa Kwamared Mustapha adamu wanda Kwamared Sa’idu Magaji Adamu ya wakilta yace; yau ranace da muka hadu a jihar Nasarawa saboda mu nunawa yan uwanmu na vangaren Shari’a cewa muna tare dasu a wanan yajin aiki da sukeyi a jihar Nasarawa.

Makasudin wanan yajin aikin shine saboda kudaden albashinsu da Babban mai Shari’a na jihar Nasarawa ya yankewa . yace ana yanke masu kudi duk wata naira miliyon hudu da dubu dari bakwai.

Daga lokacin ya zuwa yanzu an yanke kudaden Ma’aikatan yakai naira miliyon dari da casa’in . kuma sunyi kuka sun nuna damuwarsu saboda halin da ake ciki a taimaka masu a basu hskinsu. Amma ko magana mai dadi ba’ayi masu ba. Wanan ne ya sanya makasudin daukar matakin zuwa yajin aiki .

Yace; Babban alkalin jihar bai kyautawa Ma’aikatan Shari’a ba duk da cewa shine Shugaban amma baya kyautawa Ma’aikatanmu .

Kuma ma’aikata suna aikine a guri daya babu karin girma kullun a matsayi daya Mutum yake babu cigaba? Da ace ba’a cigaba a wajen aiki to da shima baikai wanan matsayin da yake ciki ba.

Ya kara da cewa batun cewa Babban Alkalin jihar Nasarawa ya kore wasu ma’aikatan Shari’a daga aiki saboda sun shiga yajin aiki to ya sani , ba haka ake koran ma’aikataba kuma basu koruba. Saboda an daukesu aiki bisa ka’idane idan za’a koresu abi ka’idoji idan sunyi lefi .

Shima da yake jawabi Shugaban kungiyar ta jihar Nasarawa Mista Musa Jimo Alengo yace; yau mun kara jaddada wanan yajin aiki saboda haka kowa yayi zamansa a gida kada ya fita zuwa ofisa .

Yace; mun samu Labarin Babban Alkalin jihar yana bi da manyan guduma yana farfasa ofisoshinmu dake rufe saboda kada ace ana yajin aiki to ya sani ba ofic bane mutani mutanine ofic idan babu wanda yazo kaga babu aiki.
Saboda haka kowa yayi zamansa babu wanda za’a koreshi a aiki. Duk da cewa suna tayin Bara zana cewa duk wanda bai koma aiki ba zasu koreshi to suyi korar mu gani ko Mutum daya bazamu bari a cimasa mutumci ba.

Idan za’a kore wani mutum daya sai dai a koremu gana daya. Kuma mun jaddada batun yajin aiki babu gudu babu jada baya. Bazamu yarda ba sai Gwamnati ta kiramu anzauna an tattauna an biyamu hakinmu sannan.

Jama’a da damane dai suka bayyana albarkacin bakinsu game da wanan yajin aikin .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here